Isra'ila: Iran Ta Umarci Jama'a Su Daina Amfani da WhatsApp, Ta Fadi Sharrin Manhajar

Isra'ila: Iran Ta Umarci Jama'a Su Daina Amfani da WhatsApp, Ta Fadi Sharrin Manhajar

  • Gwamnatin Iran, ta yi amfani da gidan talabijin dinta wajen umartar jama'a da su cire manhajar WhatsApp daga wayoyinsu saboda tsaro
  • Mahukuntan na zargin WhatsApp da tattara bayanan sirri na ‘yan kasar, kuma ta na tura su zuwa kasar Isra’ila yayin da ake gwabza yaki
  • Wannan kira ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karin tashin hankali tsakanin Iran da Isra’ila, wanda aka shiga rana ta shida ana musayar wuta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Talabijin gwamnati a kasar Iran ya bukaci al'umma su cire manhajar WhatsApp daga wayoyinsu.

Ta yi zargin manhajar na tattara bayanan masu amfani da ita domin aika su zuwa kasar Isra’ila yayin da yaki tsakanin kasashen biyu ya shiga rana ta shida.

Iran ta zargi WhatsApp da hada kai da Isra'ila
Iran ta ce Isra'ila na mika bayanan yan kasarta ga WhatsApp Hoto: WhatsApp/Getty
Asali: Facebook

Jaridar Times of Israel ta ruwaito cewa kamfanin WhatsApp ya bayyana damuwa matuka game da rahoton da ke yawo a Iran, yana mai cewa hakan zai iya zama dalilin haramta amfani da manhajar a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meta: “Ana son dakatar da WhatsApp a Iran”

Arab News ta wallafa cewa Kamfanin Meta ya nuna damuwa game da yunkurin hukumomin Iran na hana amfani da manhajar WhatsApp a fadin kasar.

Ya ce:

“Wannan rahoton karya zai iya zama dalilin dakatar da ayyukanmu a daidai lokacin da mutane ke bukatar su fiye da ko yaushe.”

Ya nanata cewa babu kamshin gaskiya a zargin da mahukuntan Iran suka yi a kan cewa ana rarraba bayanan jama'a ga Isra'ila.

Meta ta yi bayani kan tsarin tsaron WhatsApp

Meta ya ce WhatsApp na amfani da tsarin ɓoye saƙonni daga farkon aika saƙo har zuwa karshensa, wanda hakan ke nufin babu wani mai damar karanta saƙon da ake tura wa juna.

Iran na ci gaba da yaki da Isra'ila
Iran ta umarci jama'a su daina amfani da WhatsApp Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Ya ce:

“Ba ma bibiyar inda masu amfani da manhajar suke, ba ma adana bayanan wanda kake tura wa saƙo, kuma ba ma bin diddigin saƙonnin sirri da mutane ke aikawa juna."
“Ba mu bayar da bayanai ga kowanne gwamnati ba.”

Sai dai Gregory Falco, injiniya a jami’ar Cornell kuma kwararre a fannin tsaron bayanai, ya musanta ikirarin da Meta ke yi.

Ya bayyana cewa:

"An tabbatar cewa yana yiwuwa a gane wasu bayanai na WhatsApp da ba su cikin ɓoyayyen tsari da aka yiwa lakabi da encrypted metadata."

Meta ta hakikance cewa babu wanda ke iya kutsawa a cikin sakonnin jama'a saboda ta sanya su a kan tsarin boye sakonni.

Shugaban Iran ya yi martani ga Trump

A baya, mun kawo labarin cewa Shugaban Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce ƙasarsa ta shirya tsaf domin ci gaba da fafatawa da Isra’ila, yana mai cewa Iran ba za ta taɓa sassauta wa ba.

Wannan furuci ya zo ne bayan wani jawabi da shugaban ƙasar Amurka, Donald J Trump, ya yi, inda ya ce Iran ba ta da zabin da ya wuce ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba.

Trump ya kuma ƙara da cewa Amurka ta san inda Khamenei ke ɓuya, amma ba ta da niyyar kai masa hari a yanzu, lamarin da Shugaban ya ce Iran tana da cikakken shiri don kare kanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.