Majalisar Wakilai Ta Amince da Kudirorin Gyaran Haraji, An Bayyana Mataki na Gaba

Majalisar Wakilai Ta Amince da Kudirorin Gyaran Haraji, An Bayyana Mataki na Gaba

  • Majalisar Wakilai ta amince da kudirorin gyaran haraji bayan nazari daga kwamitin bai daya, ƙarƙashin jagorancin Abbas Tajudeen
  • Daya daga cikin manyan batutuwa da aka amince da su shi ne tsarin rabon VAT da kuma kin amincewa da karin VAT din zuwa kashi 10%
  • Sai dai, duk da amincewar majalisar wakilan, har yanzu kudurorin ba su zama doka ba, ana jiran amincewar majalisar dattawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja, na nuni da cewa majalisar wakilai ta amince da kudirorin gyaran dokokin haraji huɗu a ranar Alhamis.

An amince da kudirorin ne bayan nazari da tantancewa daga kwamitin bai daya, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisa, Abbas Tajudeen.

Majalisar wakilai ta amince da kudirorin gyaran haraji
Majalisar ta amince da kudirorin gyaran haraji, an mika su ga majalisar dattawa. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Majalisa ta amince da kudirorin gyaran haraji

Mai magana da yawun shugaba kasa, Bayo Onanuga, a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce yanzu za a jira amincewar majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Biyan haraji: Majalisa ta yi wa sojoji gata, an gabatar da muhimmin kudiri a gabanta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kwamitin da ya kula da rahoton ya gyara sassan da suka jawo ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa aka amince da kudirorin cikin sauki.

Daya daga cikin muhimman batutuwa da aka amince da su shi ne tsarin rabon VAT bisa kashi 50% na daidaito, 20% na yawan jama'a, da 30% cinikayyar da aka yi a jiha.

Majalisa ta soke batun karin harajin VAT

Majalisar ta yi watsi da shawarar duba yiwuwar ƙarin kudin VAT a lokaci zuwa lokaci, inda ta amince a ci gaba da amfani da kashi 7.5% na yanzu.

Majalisar ta goge kalmar “ecclesiastical” (da ke nufin coci ko malamin coci) daga ɗaya daga cikin sassan kudirin saboda rashin fahimta, tare da maye gurbinta da “religious” watau 'addini'.

Har ila yau, ta amince da ci gaba da bai wa asusun TETFUND, hukumar NASENI, da NITDA tallafin kudin gudanarwa daga daga kudaden haraji.

Kara karanta wannan

An gano shugaban kasar da ya kafa kungiyar Lakurawa da yadda suka shigo Najeriya

An kuma gyara sashe mai cin karo da juna kan harajin gado, inda aka bayyana cewa dukiyar da aka gada kafin rabuwar iyali ba za a sanya mata haraji ba.

Wasu daga cikin sauye-sauyen da aka samu

Majalisar wakilai ta yi wasu gyare-gyare a kudirorin gyaran haraji da Tinubu ya gabatar
Majalisar wakilai ta amice da kudirorin gyaran haraji bayan 'yan gyare-gyare. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Majalisar Wakilai ta amince da rahoton kudirin doka da ke tsara hanyoyin tantancewa, karɓa, da kula da kudaden shiga na tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Kudirin ya kuma fayyace ikon hukumomin haraji da ayyukansu, tare da samar da doka da za ta tabbatar da gudanar da harkokin haraji yadda ya kamata.

An amince da kudirin da ke neman soke dokar kafa Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS) da samar da Hukumar Haraji ta Najeriya don kula da kudaden shiga.

Bugu da ƙari, majalisar ta amince da kudirin kafa hukumar haraji ta haɗin gwiwa, kotun korafe-korafen haraji, da ofishin kare hakkin masu biyan haraji.

Wannan kudirin yana nufin haɗa dokokin haraji daban-daban domin samun daidaito, da samar da doka guda da za ta tsara haraji a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Duk da amincewar majalisar wakilai, har sai an jira majalisar dattawa ta amince da kudirorin ne sannan za su iya zama doka.

Majalisa ta yi zama na musamman kan gyaran haraji

Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar wakilai za ta gudanar da nazari mai zurfi kan rahotannin kudirin gyaran haraji da kwamitin sauraron ra’ayoyin jama’a ya tattara.

Kakakin majalisa, Abbas Tajudeen, ya bukaci dukkan ‘yan majalisa su halarta domin tabbatar da an tantance ra’ayoyin jama’a yadda ya kamata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng