'Ba Mu Muka Yi ba,' Gwamnatin Katsina Ta Yi Bayanin 'Yarjejeniya' da Yan Bindiga

'Ba Mu Muka Yi ba,' Gwamnatin Katsina Ta Yi Bayanin 'Yarjejeniya' da Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa tana nan daram a kan bakarta na kin neman sulhu da yan ta'adda da suka addabi jama'a
  • Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu ya ce wadanda aka gani an yi sulhu da su a jihar, su ne suka kawo kansu
  • Ya kara da cewa duk da gwamnati ba za ta nemi kowane dan bindiga ba, amma za a ba wadanda suka kawo kansu damar sulhu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta jita-jitar cewa tana kokarin sulhu da ‘yan bindiga, bayan da wani rahoto ya karade kafafen yada labarai cewa an cimma yarjejeniyar zaman lafiya da su.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Dikko Radda na kan bakanta na yakar rashin tsaro.

Gwamnan Katsina, Dikko Radda
Gwamnatin Katsina ta musanta neman sulhu da yan bindiga Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa yan ta'addan da aka ga sun zauna da gwamnati, sun mika wuya ne don radin kansu domin wanzuwar zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishina: "Tsaron rayuka ne burin gwamnatin Katsina"

The Guardian ta wallafa cewa Kwamishinan tsaron cikin gida a Katsina, Nasir Mu'azu ya tabbatar da cewa gwamna Dikko Radda ba zai sassauta ra'ayinsa a kan yaki da yan ta'adda ba.

Nasir Mu’azu ya bayyana cewa:

“Kowa ya san cewa Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya yi alkawarin cewa tsaro shi ne babban burinsa. Kuma ya nuna hakan a aikace tare da jajircewarsa wajen magance matsalar rashin tsaro baki daya.”
“Muna da kananan hukumomin da ke gaban gaba da barazanar hare-haren ‘yan bindiga, ciki har da Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume da wasu da dama – kusan 10 ko 11 ne gaba daya.”

Gwamnan Katsina bai neman sulhu da 'yan bindiga

Kwamishinan ya jaddada cewa Gwamna Dikko Radda yana kan bakansa na kin amincewa da sulhu da ‘yan bindiga, kuma wannan matsaya na nan har yanzu.

Gwamnatin Katsina ta ce za ta kare rayukan jama'a
Gwamnatin Katsina ta gargadi tubabbun yan ta'adda Hoto: Umaru Dikko Radda
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan bindigar da aka gani cikin tayin zaman lafiya su ne da kansu suka yanke shawarar ajiye makamansu domin ba zaman lafiya dama.

Ya ce:

“Mun shafe fiye da shekaru biyu muna fafatawa da ‘yan bindiga, kuma da taimakon Allah muna samun nasarori. Gwamnatin jihar Katsina a karkashin Malam Dikko Umar Radda ta bayyana a fili cewa ba za ta zauna da ‘yan bindiga ba, sai dai idan su da kansu suka ajiye makamansu, za a basu damar zaman lafiya.”
“Ina so in fayyace cewa gwamnatin Katsina tana nan a kan matsayarta, ba ma sulhu da ‘yan bindiga. Amma idan suka ajiye makamansu, za mu ba su damar zama ‘yan kasa nagari a cikin jihar.”

Katsina: Gwamnati ta gargadi tubabbun yan bindiga

A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta gargaɗi tubabbun ’yan bindiga da suka amince su ajiye makami da komawa zaman lafiya da su cika alkawari.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, da yayi gargadin ya ce duk wanda aka kama ya koma ruwa zai fuskanci kakkausan martani daga gwamnati da jami'ai.

Kwamishinan ya kara da cewa wasu daga cikin shugabannin ’yan bindiga a ƙananan hukumomin Jibia, Batsari da DanMusa sun yanke shawarar ajiye makami don kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.