Shirin da Gwamnatin Katsina Ke Yi Wa Tubabbun 'Yan Bindiga

Shirin da Gwamnatin Katsina Ke Yi Wa Tubabbun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Katsina ta fara shirye-shiryen ilmantar da tubabbun ƴan bindigan da suka ajiye makamansu
  • Hukumar kula da ilmin manyan mutane ta bayyana cewa za ta samar da azuzuwan da za a riƙa koyar da irin waɗannan mutanen
  • Ta bayyana cewa hakan zai taimaka wajen yunƙurin da ake yi na sake dawo da su a cikin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Hukumar kula da Ilmin manyan mutane ta jihar Katsina ta bayyana shirin fara azuzuwan koyon karatu ga tsofaffin ƴan bindiga da suka tuba.

Hukumar ta bayyana cewa hakan wani yunƙuri ne na dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata.

Gwamnatin Katsina za ta saka tubabbun 'yan bindiga a makaranta
Gwamnatin Katsina za ta samar da azuzuwa don tubabbun 'yan bindiga Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ce gwamnatin jihar ta bayyana cewa wannan shiri ya biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a wasu ƙananan hukumomi da rikicin ƴan bindiga ya addaba a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan dai sun miƙa makamansu da kansu yayin tattaunawar zaman lafiya, da nufin dawo da zaman lafiya a yankunan da rikicin ya shafa.

Za a maida tubabbun ƴan bindiga makaranta

Da take magana da manema labarai a Katsina, shugabar hukumar ilmin manyan mutane ta jihar Katsina, Bilkisu Muhammad Kakai, ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirya tura malamai domin gudanar da waɗannan azuzuwan.

Ta ƙara da cewa shirin zai haɗa da koyar da ilmin addinin Musulunci da kuma na zamani domin gyara ɗabi’u da rayuwar tsofaffin ƴan bindigan da suka tuba, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Za mu yi aiki tare da shugabannin ƙananan hukumomi domin buɗe azuzuwan ɗaya bayan ɗaya. Babban abin da za a mayar da hankali a kai shi ne ilmin addini da kuma na zamani."

- Bilkisu Muhammad Kakai

A yayin da take duba nasarorin da hukumar ta samu cikin watanni shida da suka gabata, Bilkisu Muhammad Kakai ta bayyana cewa an kafa sababbin azuzuwan karatun manya guda 68 a gundumomin jihar.

Haka zalika, ta bayyana cewa an buɗe aji na koyon karatu a matakin farko a gidan gyaran hali na Katsina domin taimaka wa fursunoni da ke da burin ci gaba da karatu har zuwa jami’a.

Ta ce wannan aji an shirya shi ne don bai wa fursunoni damar ci gaba da karatu da kuma samun shiga jami’a domin samun takardar digiri.

Ta kuma bayyana cewa ta ziyarci dukkan ƙananan hukumomi a jihar domin duba azuzuwan karatun manya da cibiyoyin koyar da mata, da kuma tantance halin da suke ciki.

Gwamnatin Katsina za ta koyar da tubabbun 'yan bindiga
Za a samar da azuzuwan koyar da tubabbun 'yan bindiga a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Gwamna Radda ya samu yabo

Ta yabawa Gwamna Dikko Umar Radda bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar, tare da bayyana cewa an ware kuɗaɗe a kasafin kuɗi na bana domin magance matsalolin da cibiyoyin ke fuskanta.

Sai dai ta roƙi wakilan jihar a majalisar tarayya da su haɗa gwiwa da hukumar domin kafa ƙarin cibiyoyin karatun manya da na mata a mazaɓunsu.

Ƴan bindiga ba su da amana

Tukur Lawal ya shaidawa Legit Hausa cewa duk da cewa shirin abu ne mai kyau amma ƴan bindiga ba abin yarda ba ne.

"Ina ganin indai har shirin ya tafi yadda ya kamata zai taimaka wajen sauya musu tunani."
"Da yawa daga cikinsu ba su da ilmin addini ballantana na boko. Idan suka samu ilmi tunaninsu zai sauya kan yadda za su riƙa kallon rayuwa."
"Allah ya su yi tabbatacciyar tuba ba tubar muzuru ba."

- Abubakar Salisu

Ɗan bindiga ya jagoranci zaman sulhu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hatsabibin ɗan bindiga, Ado Aliero, ya jagoranci wani zaman sulhu a jihar Katsina.

Ado Aliero ya jagoranci zaman sulhun ne a ƙaramar hukumar Danmusa domin a samu zaman lafiya mai ɗorewa.

Zaman sulhun dai na zuwa ne yayin da jami'an tsaro suke farautar tantirin ɗan bindigan da ya daɗe yana addabar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng