Abin Ya Juya: An Shiga Firgici a Kano da Ango Ya Hallaka Amaryarsa da Wuƙa

Abin Ya Juya: An Shiga Firgici a Kano da Ango Ya Hallaka Amaryarsa da Wuƙa

  • A ranar Talata, an samu mummunan labari a karamar hukumar Gwarzo a Kano, inda wani matashi ya hallaka sabuwar amaryarsa
  • Lamarin ya faru bayan sallar Azahar, inda aka gano mamaciyar da munanan raunuka a wuya da cinyarta cikin jini a daki
  • Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa lamarin ya girgiza 'yan garin Gwarzo wanda ya sa mutane tambayar silar faruwar haka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani mummunan lamari ya afku a jihar Kano da ya ta da hankulan al'umma da ke zaune a yankin.

A ranar Talata, an sake shiga tashin hankali a layin Minista a karamar hukumar Gwarzo, Jihar Kano, bayan ango ya hallaka amaryarsa.

Ango ya yi ajalin amaryarsa a Kano
Sabon ango ya hallaka amaryarsa a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Rahoton Aminiya ya tabbatar da cewa ma'auratan kwata-kwata ba su wuce wata 2 ba da yin aure a Gwarzo da ke jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake samun kashe-kashe tsakanin ma'aurata

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun kisan amarya ko ango a Arewacin Najeriya da ma fadin kasar baki daya.

Akwai dalilai da dama da ake zargin suna haddasa hakan wanda suka haɗa da auren dole daga ɓangaren matan.

Wasu na ganin cikin dalilan akwai sabani da ake samu tsakanin sababbin auren na yau da kullum ba tare da sanin cewa duka zaman aure hakuri ba ne.

Yadda ango ya hallaka amaryarsa a Kano

An tabbatar da cewa matashin da ake zargi ya kashe sabuwar amaryarsa ta hanyar yanka ta da wuka wanda ya yi sanadin rasa ranta.

Majiyoyi suka ce lamarin ya tayar da hankulan al'umma baki daya da ke yankin tare da sanya musu shakku.

An ce abin ya faru da rana tsaka bayan sallar Azahar, inda aka samu mamaciyar da munanan raunuka a wuyanta da cinyarta.

Yadda ango ya aika amaryarsa lahira a Kano
Ango ya yi ajalin amaryarsa a Kano. Hoto: Legit.
Asali: Original

Kano: Dalilin zargin ango da kisan amarya

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mijinta ake zargi da kisan, domin shi ma an same shi da raunuka a hannunsa, alamar yankan wuka.

Wani mutumi a yankin, wanda ya bukaci a boye sunansa ya nuna takaici kan lamarin da ya afku tare da nuna fargaba kan dalilin faduwar haka.

Mutumin ya ce:

“Wallahi, wannan abu ya girgiza Gwarzo, aurensu bai wuce wata daya da sati guda ba."

Ya kara da cewa, mutane da dama sun taru a kofar gidan suna kuka da firgici, suna tambayar me ke janyo irin wannan ta’asa tsakanin ma’aurata.

Wasu na ganin soyayya ce ta rikice, yayin da wasu ke alakanta lamarin da rashin tarbiyya da sakacin da ke tsakanin sababbin ma’aurata da iyayensu.

Amarya ta kashe angonta a jihar Kano

Mun ba ku labarin cewa mutane sun shiga tashin hankali a Kano yayin da wata amarya, Saudat Jibrin ta daba wa angonta Salisu Ibrahim wuka har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa an daura auren Saudat da Salisu a ranar 27 ga Afrilun 2025 kuma amaryar ta kashe angonta a darensu na tara.

Wani ganau ya ce Saudat ta yanka Salisu a wuya bayan ta nemi ya rufe idonsa da sunan za su yi wasa inda ya mutu bayan an kai shi asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.