Marigayi Yar'Adua da Sauran Manyan Ƙasa da Tinubu Ya Gwangwaje da Lambar Yabo
- Shugaba Bola Tinubu ya ba marigayiya Kudirat Abiola, Janar Shehu Musa Yar’Adua da Farfesa Humphrey Nwosu lambar yabo
- Wole Soyinka da Janar Akinrinade sun samu lambar yabon GCON, yayin da Bola Ige, Balarabe Musa da sauransu suka samu CFR
- Tinubu ya ce za a saki cikakken jerin waɗanda aka karrama nan gaba, ciki har da sabbin sunaye da suka taimaka wa ci gaban ƙasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis ya ba marigayiya Kudirat Abiola, Shehu Musa Yar’Adua da Humphrey Nwosu lambar yabo ta ƙasa.
Wadannan lambobin yabo sun zo ne sakamakon rawar da suka taka wajen samar da dimokuraɗiyya a Najeriya a lokutan mulkin soja.

Asali: Facebook
Tinubu ya ba Yar'adua, Soyinka lambobin yabo
Hakan na cikin wata sanarwa da shafin shugaban kasar ya wallafa a X a yau Alhamis 12 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadiminsa, Sunday Dare ya ce Tinubu ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa na ranar dimokradiyya a yau Alhamis 12 ga watan Yunin 2025.
Marigayiya Kudirat Abiola, matar MKO Abiola wanda ake tunanin ya lashe zaɓen 12 ga Yuni, 1993, ta samu lambar CFR daga gwamnatin Tinubu
Janar Shehu Musa Yar’Adua, babban ɗan’uwan tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua, ya samu mafi girman lambar yabo ta GCFR.
Shugaba Tinubu ya sanar da hakan ne yayin jawabin bikin ranar Dimokuraɗiyya a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Ɗinkin Tarayya.
Wadanda aka karrama saboda gwagwarmayar tabbatar da sakamakon zaɓen Yuni 12 sun haɗa da Farfesa Wole Soyinka da Janar Alani Akinrinade.
Su biyun sun samu GCON, lambar yabo ta biyu mafi girma a ƙasa, saboda irin rawar da suka taka wajen kare demokuraɗiyya.
Marigayi Bola Ige, Balarabe Musa, Alfred Rewane, Frank Kokori da wasu su ma sun samu CFR a matsayin karramawa.

Asali: Twitter
Sauran wadanda suka samu lambar yabo
Sauran sun hada da Alao Aka-Bashorun, Fredrick Fasheun, Polycap Nwite da Sanata Ayo Fasanmi da suka taka rawar gani.
Haka kuma an karrama Olatunji Dare, Bayo Onanuga, Dare Babarinsa da Sanata Shehu Sani da lambar yabo ta CFR.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Lauyan kare haƙƙin bil’adama Femi Falana da Sanata Tokunbo Afikuyomi suma sun shiga jerin.
Sauran sun hada da Seye Kehinde, Olawole Osun, Farfesa Segun Gbadegesin da Farfesa Julius Iyorbere na Majalisar Wakilai.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa za a fitar da cikakken jerin wadanda aka karrama da lambobin yabo nan gaba kadan.
An roki Tinubu ya dawo da Fubara kan mulki
Mun ba ku labarin cewa jigon PDP ya bukaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yafewa Siminalayi Fubara kamar yadda ya yafewa Babajide Sanwo-Olu a Lagos.
Cif Bode George ya ce maido da Fubara zai nuna girmamawa ga waɗanda suka yi sadaukarwa don assasa dimokuraɗiyya a Najeriya.
A ranar 18 ga Maris ne shugaban kasa, Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers tare da dakatar da gwamna, Fubara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng