Matar Sanata Ta Shiga Matsala, Kotun Ingila na Tuhumarta da Halasta Kudin Haram

Matar Sanata Ta Shiga Matsala, Kotun Ingila na Tuhumarta da Halasta Kudin Haram

  • Wata kotu a Birtaniya ta bayar da umarnin kwace kadarar da Abigail Katung, matar Sanata Sunday Katung mai wakiltar Kaduna ta Kudu
  • An bayyana cewa kadarar mallakin wani attajirin dan kasuwa ne mai suna Mansoor Hussain, wanda ake zargi da safarar kudaden haram
  • Binciken kotun Ingila ya nuna shakku kan yadda aka biya wani kaso a cikin kudin gidan da matar Sanatan ta ce mijinta ne ya ba ta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Britain– Babbar kotu da ke King's Bench Division a ƙasar Birtaniya ta ba da umarnin kwace wata kadarar da shugabar birnin Leeds, kuma matar Sanatan Najeriya, Abigail Katung ke zaune a ciki.

Kotun ta umarci hukumar yaki da manyan laifuffuka (NCA) ta Birtaniya da ta kwace kadarar da aka ce wani attajirin ɗan kasuwa mai suna Mansoor Hussain ne ya mallaka tun farko.

Ana shari'a da matar Sanatan Najeriya a Igila
Matar Sanatar Kaduna na fuskantar shari'a a Ingila Hoto: Abigail Marshall Katung/Nigerian Senate
Asali: Facebook

A wani rahoto da ya kebanta ga Premium Times ta wallafa ya bayyana cewa, a baya, jami’ai sun zargi Hussain da halasta kudin haram na manyan shugabannin kungiyoyin masu aikata laifuka a Arewacin Ingila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ingila: Matar Sanatan Najeriya ta samu matsala

Abigail Katung, matar Sanata Sunday Katung wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, na zaune a gidan tare da yaranta biyu.

Tun a shekarar 2015, wacce ita ce shekarar da mijinta ya fara zama ɗan majalisar wakilai, ta sanya hannu kan yarjejeniyar siyan gidan daga hannun Hussain a kan £1,000,000

A cikin yarjejeniyar, Katung ta biya £400,000 a matsayin na kuɗin siyan gidan, inda ta biya £40,000 da farko sannan daga baya ta cika £360,000 ga Hussain.

Ana zargin matar Sanata da aikata laifi

Takardun da kotun Birtaniya ta gabatar sun nuna cewa akwai alamun ana halasta kudin haram a cikin ragin kuɗin da Katung ta biya a watan Afrilu zuwa Mayu na 2015.

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan an zaɓi mijinta a matsayin Sanata da kuma kafin rantsar da shi a watan Yuni.

Ana zargin matar Sanata da halasta kudin haram
Matar Sanata ta ce mijinta ne ya ba da kudin sayen wani gida a Ingila Hoto: Nigerian Senate
Asali: UGC

Kotun ta gudanar da bincike kan asalin kuɗin £360,000 da aka ce sun fito daga Najeriya, inda Katung ta bayyana yadda ta canja kudin.

Rahoton ya ce kotun ta ce wasu daga cikin kuɗin, mijinta ne ya samo su daga Najeriya.

Sanatoci, 'yan majalisa sun sauya sheka

A baya, mun ruwaito cewa guguwar canji na ci gaba da kadawa a fagen siyasar Najeriya, inda 'yan majalisar tarayya 12 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar mai mulki ta APC.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake zargin APC na neman janyo gwamnonin PDP da sauran manyan 'yan adawa zuwa cikinta a kokarinta na tunkarar babban zaben 2027 mai zuwa.

'Yan majalisar tarayya guda 10 daga jihar Akwa Ibom, wadanda aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyun PDP da YPP, sun yanke shawarar komawa APC tare da Gwamna Umo Eno.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.