Juyin Mulki: Ministan Tsaro Ya Bayyana Yadda Aka Yaudari Kananan Sojoji

Juyin Mulki: Ministan Tsaro Ya Bayyana Yadda Aka Yaudari Kananan Sojoji

  • Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya kuma sake gargadi game da yunkurin juyn mulki a Najeriya inda ya fadi hukuncin da ke cikin haka
  • Ya ce sojoji da ‘yan ƙasa suna goyon bayan dimokiraɗiyya, kuma an riga an hana duk wani yunƙurin kifar da gwamnatin farar hula
  • Janar Musa mai ritaya ya ce binciken yunƙurin juyin mulki da aka yi ya kammala, kuma ana ci gaba da shari’a kan waɗanda ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya yi gargadi mai tsauri game da yunkurin juyin mulkin gwamnatin Bola Tinubu.

Musa ya bayyana cewa duk wanda ke tunanin shirya juyin mulki a Najeriya yana ɓata lokacinsa ne, yana mai cewa ‘yan kasar za su tunkari duk wani yunƙuri na kifar da tsarin dimokiraɗiyya.

Kara karanta wannan

'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki

Ministan tsaro a bayyana tasirin dimukradiyya a Najeriya
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

A yayin wata hira da Arise TV, Musa ya ce dimokiraɗiyya ta fi mulkin soja kyau, kuma rundunar sojoji na kare tsarin mulkin ƙasa.

Ministan tsaro ya soki yunkurin juyin mulki

Ministan ya ce ya taba shiga binciken wani yunƙurin juyin mulki inda shi da wasu manyan hafsoshi suka gano tare da kai rahoto kan lamarin.

Musa ya bayyana waɗanda ake zargi da shirin juyin mulki a matsayin “rikitattun mutane” da suka yaudari ƙananan hafsoshi suka shiga aikin.

Ya ƙara da cewa sojoji na samun kulawa sosai, babu matsalar albashi, kuma ana ƙara inganta alawus da kayan aiki don yaƙar rashin tsaro.

Ministan tsaro ya bayyana hukuncn da ke jiran masu hannu a yunkurin juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu da aka yi yunkurin yi masa juyin mulki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

'Yan Najeriya za su hana juyin mulki'

Ministan ya tabbatar cewa duk wani yunƙurin juyin mulki ba zai yi nasara ba, yana mai cewa har fararen hula ma za su tunkare su, cewar Daily Post.

Ya ce:

“Duk wanda ke tunanin yin juyin mulki yana ɓata lokacinsa, har ma fararen hula a Najeriya za su dakatar da su.”

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Ya bayyana cewa binciken da aka yi ya kasance mai zurfi, kuma shari’a da kotun soja na ci gaba da tafiya.

Yadda gwamnati ke kokarin inganta tsaro a Najeriya

Tsohon hafsan sojan ya ce an ba waɗanda ake tuhuma damar kare kansu, kuma ana bin dukkan matakai na doka ba tare da ɓoye komai ba.

Musa ya ce babu dalilin da zai sa a yi juyin mulki, yana mai cewa sojoji da gwamnati na aiki sosai wajen inganta tsaro da jin daɗin jama’a.

Ya jaddada cewa Najeriya na ci gaba, kuma duk wanda ke tunanin kifar da gwamnati zai fuskanci gazawa da turjiya mai ƙarfi.

Yadda aka tsara harbe Ministan tsaro

An ji cewa Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa yana cikin mutanen da masu yunkurin juyin mulki suka sanya a jerin waɗanda za a harbe.

Janar Musa mai ritaya ya ce wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane ma na daga cikin waɗanda aka tsara kashewa a yunkurin juyin mulkin.

Ya yi bayani ne bayan sojoji sun tabbatar da cewa jami’an da ake zargi za su fuskanci shari’a a gaban kotun soja bisa tanadin dokokin aikinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.