Abin da Ba a Taba Yi Ba: Dan Najeriya Ya Kafa Tarihi a Duniyar Wasan ‘Chess’, Tinubu Ya Yaba Masa

Abin da Ba a Taba Yi Ba: Dan Najeriya Ya Kafa Tarihi a Duniyar Wasan ‘Chess’, Tinubu Ya Yaba Masa

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa matasan Najeriya na da juriya da fikira a yunkurinsu na ganin sun taka rawar gani a duniya
  • Tinubu, a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi iyakar kokarinta wajen tabbatar da cewa ta himmatu wajen samar da damammaki ga matasan kasar
  • Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ya yabawa Tunde Onakoya wanda ya kammala aniyarsa ta kada tarihi a kudin duniya a wasan 'chess' a a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya taya Tunde Onakoya murnar kafa sabon tarihi a duniya tare da nuna jajircewar Najeriya da juriya , da hazakar matasa a duk inda suka tsinci kansu a duniya.

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Abubuwan da gwamnati ta shirya yi a bikin cikar Tinubu shekara 1 a mulki

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu, ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, Tinubu ya yaba wa Onakoya bisa irin wannan bajintar da ya yi.

Tinubu ya taya mai wasan chess murnar kafa tarihi
Yadda dan Najeriya ya kafa tarihi, Tinubu ya taya shi murna | Hoto: @Kehinde_Slitz
Asali: Twitter

Hakazalika, ya yaba masa musamman ganin irin kwarin gwiwar da ke tattare da shi na tara kudade domin tallafawa yara a nahiyar Afirka su koya da kuma samun dama ta hanyar darar ‘chess’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al’adar ‘yan Najeriya ne jajircewa, inji Tinubu

Shugaban ya yi nuni da cewa matashin ya nuna al’adar matasan Najeriya ta jajircewa wajen ganin sun samu sauyi mai kyau a fannoni da yawa na rayuwa.

Shugaban buga misalin da Onakoya wajen jinjina wa jajircewar da matasan kasar ke wajen ganin sun tabbatar da sunan Najeriya ya daga a duniya.

A cewar Shugaba Tinubu:

“Matasan Najeriya sun nuna a kowanne fanni, ciki har da wakokin Afrobeats, Nollywood, masana’antu masu tasowa, ilimi, kimiyya, da fasaha, cewa sannu a hankali komai ke girma.”

Kara karanta wannan

Babu tabbacin dawo da kudin tallafin wutar Lantarki Inji NERC

Tinubu ya tabbatarwa da ‘yan kasar nan cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen fadada samar da damammaki ga matasa don tabuka abin a zo a gani a kasa da ma wajenta.

Yaro dan Najeriya ya fara suna a wasan ‘chess’

Ba wannan ne karon farko ba, a baya kun ji yadda Tanitoluwa Adewumi, wani yaro ne dan Najeriya mai shekaru 8 a duniya, da iyayensa suka tattara su ka koma kasar Amurka ya kafa tarihi a was an ‘chess’.

Yaron, wanda iyayensa suka koma Amurka bayan ‘yan ta’addan Boko Haram sun fitine su, yanzu ya zama abin misali a was an.

Mun rahoto maku yadda yaron a cikin shekaru kadan yak ware a wasan mai bukatar tsananin tunani da mai da hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel