Tinubu na Shan Kakkausar Suka kan Sanya wa Dakin Taron da IBB Ya Gina Sunan Shi

Tinubu na Shan Kakkausar Suka kan Sanya wa Dakin Taron da IBB Ya Gina Sunan Shi

  • Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da sabunta dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja tare da canza sunan shi zuwa Bola Ahmed Tinubu ICC
  • Tinubu ya yabawa Ministan Abuja, Nyesom Wike, bisa jagoranci da kulawa wajen gyaran ginin da ya ce ya zama abin alfahari ga Najeriya
  • Sai dai fitattun ‘yan Najeriya da dama sun soki matakin, suna cewa bai dace shugaban kasa ya sa sunansa a ginin da ba shi ya yi ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A ranar Talata, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da gyaran dakin taro na kasa da kasa da ke birnin Abuja.

Legit ta gano cewa an sabunta sunan dakin taron zuwa Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre.

An saka wa ICC sunan Tinubu
Tinubu na shan suka kan saka wa ICC sunan shi. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Wasu fitattun mutane a Najeriya sun soki matakin da aka dauka na sauya sunan dakin taron, kamar yadda Hakeem Baba Ahmed ya wallafa sakon sukar matakin a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ce ce sabunta dakin taron ya nuna jajircewar gwamnatinsa wajen inganta abubuwan more rayuwa.

Shugaban kasar ya jinjina wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, bisa jajircewa da kulawa da ya nuna wajen ganin aikin ya kammala.

An soki matakin sakawa ICC sunan Tinubu

Daya daga cikin wadanda suka soki wannan mataki shi ne Hakeem Baba-Ahmed, wanda ya bayyana cewa bai kamata Tinubu ya amince a saka sunansa a cibiyar ba.

A cewarsa:

“Shugabanni sukan samu karramawa ne bayan sun yi ayyukan da suka cancanci yabo.
"Wannan matakin da aka dauka ba shi da alamar kaskantar da kai ko sadaukarwa – halaye da shugabanni nagari ke da su.”

Shehu Sani ya ce IBB ya fi cancanta da ICC

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa an gina dakin taron ne ne a zamanin tsohon Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).

A karkashin haka ya wallafa a Facebook cewa shi ya fi dacewa da a saka sunan shi idan har akwai bukatar hakan.

Shi ma wani mai sharhi, Abubakar Widi-jalo, ya wallafa a Facebook cewa:

“Sanya sunan ICC da sunan Tinubu wata babbar dabarar siyasa ce, kuma ina da yakinin cewa duk wanda ya gaje shi zai mayar da sunan ginin kamar yadda ya ke kafin hakan.”
Tinubu yayin bude ICC
Wike da Tinubu yayin bude ICC a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Ya ce da a ce Tinubu ya saka sunansa a titin Legas zuwa Calabar da gwamnatinsa ke ginawa, hakan ba zai jawo ce-ce-ku-ce ba, domin aikin gwamnatinsa ne daga tushe.

Wasu na ganin cewa sabunta ginin kadai bai isa dalili ba na canza masa suna zuwa na shugaban kasa da ke kan mulki, musamman da yake ginin na da tarihi mai zurfi tun zamanin mulkin soja.

Yadda ake sukar Bola Tinubu da shugabancinsa

Tun daga ranar da Bola Ahmed Tinubu ya hau kujerar shugaban ƙasa a watan Mayu 2023, ya fuskanci suka daga sassa daban-daban na al’ummar Najeriya.

Yayin da wasu ke kallon matakan da yake ɗauka a matsayin gyara ko farfaɗowa ga tattalin arziki da shugabanci, da dama daga cikin ‘yan ƙasa na ganin sauye-sauyen nasa sun fi cutar da talaka fiye da amfanarsa.

Matakin cire tallafin mai na ɗaya daga cikin abubuwan da suka haddasa gagarumar matsin rayuwa, hauhawar farashin abinci, da karancin kudin shiga ga iyalai da yawa.

Wannan ya sa jama’a ke ci gaba da caccakar gwamnatin Tinubu, suna zargin rashin tausayi da tsare-tsaren da ba su dace da halin da mutane ke ciki ba.

Haka kuma, wasu daga cikin matakan nadin mukamai da tsarin albashi da kwangila sun kara sa jama’a shakku kan adalcin gwamnatin.

Duk wani sabon mataki da shugaba Tinubu ke ɗauka – kamar canza sunan muhimman gine-gine ko amfani da sunansa – yana jawo ce-ce-ku-ce da suka daga masu sharhi da ƙwararru.

Yayin da Tinubu ke ƙoƙarin kafa tarihinsa, ana ci gaba da kallon gwamnatinsa da idon bincike da tambaya: Shin gyaran ne ko nuna iko?

Obi ya soki tsare tsaren Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a LP a 2023, Peter Obi ya soki salon tafiyar Bola Tinubu.

Peter Obi ya ce Bola Tinubu bai bi hanyar da ta dace ba wajen cire tallafin man fetur a lokacin rantsar da shi.

Jagoran LP a Najeria ya bayyana matakan tattali da zai dauka da ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng