Da Gaske an Jefi Sarki Sanusi II da Dutse a Hawan Sallah a Kano? An Samu Bayanai

Da Gaske an Jefi Sarki Sanusi II da Dutse a Hawan Sallah a Kano? An Samu Bayanai

  • Wani abu mai tayar da hankali ya faru a Kano yayin da wata na'ura ta faɗo kusa da Sarki Muhammadu Sanusi II a yayin jawabinsa a fadar gwamnati
  • Da farko, jita-jita ta yadu cewa an jefa masa dutse ne, amma daga baya mai sarrafa na'urar daukan hoto a wajen ya bayyana gaskiyar lamarin
  • Mai daukar hoton, Salim Ameenu, ya ce na’urarsa ce ta faɗo saboda matsalar batir, kuma ya nemi gafarar Mai Martaba Sarki bisa abin da ya faru

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wani abin ban mamaki ya faru yayin bikin Hawan Nasarawa a Kano, inda wata na'ura ta faɗo kusa Sarki Muhammadu Sanusi II yana gabatar da jawabi a fadar gwamnati.

Bayan faruwar lamarin, wani bidiyo ya karade kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka rika bayyana ra’ayoyi daban-daban, har ma da zargin cewa an jefi sarkin da dutse.

An samu bayani kan zargin jifan Sanusi II a Kano.
Mai daukar hoto ya musa jifan Sanusi II yayin hawan Nasarawa. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Sai dai wanda yake aikin daukar hoto a lokacin, Salim Ameenu ya bayyana gaskiyar abin da ya faru a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salim Ameenu ya tabbatar da cewa ba dutse aka jefa ba, illa dai wata na’ura mai shawagi (drone) ce ta faɗo saboda matsalar baturi.

Jifan Sanusi II: Mai daukar hoto ya magantu

Jaridar the Guardian ta wallafa cewa Salim Ameenu da ke sarrafa na’urar ya bayyana cewa na’urarsa ce ta faɗo, kuma ba da gangan ba hakan ya faru ba.

A cewarsa:

“Jiya ina sarrafa na'ura ta, ta zagaya inda Mai Martaba ke jawabi yayin Hawan Nasarawa. Saboda matsalar batir, na rasa ikon sarrafa ta, kuma hakan ya sa ta faɗo kusa da shi.”

Ya kara da cewa abin da ya fi burge shi shi ne yadda Sarkin ya ci gaba da jawabinsa ba tare da firgita ko dakatawa ba, yana mai yabawa da kwanciyar hankalin da ya nuna.

An yi jita-jita saboda rikicin sarautar Kano

Tun bayan faruwar lamarin, wasu rahotanni sun alakanta faɗuwar na'urar da rikicin masarautar Kano, inda yanzu haka akwai sarakuna biyu da ke ikirarin zama Sarki.

Sarki Sanusi II ya dawo kan karagar mulki ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soke nadin da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya yi wa Sarki Aminu Ado Bayero.

An ba Sanusi Hakuri kan matsalar da aka samu yayin hawan sallah
An ba Sanusi Hakuri kan matsalar da aka samu yayin hawan sallah. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Wannan mataki ya haddasa rudani a jihar, inda yanzu haka Sanusi II ke zama a babban fadar Kano, yayin da Aminu Ado ke zama a wata karamar fadar daban da ke unguwar Nasarawa a cikin birnin.

A ƙarshe, Salim Ameenu ya nemi gafarar Sarkin da al’ummar Kano gaba ɗaya, yana mai bayyana cewa zai dauki matakan tsaro na gaba don kada irin wannan lamarin ya sake faruwa.

Rikice-rikicen da ke dabaibaye da Sarki Sanusi

Tun kafin sauke shi daga karagar mulki a 2020, Sarki Muhammadu Sanusi II ya sha jawo cece-kuce da mahawara a Arewacin Najeriya saboda irin salon mulkinsa da ra’ayoyinsa.

Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya kasance mai sukar al’adu da dabi’un da ke hana ci gaban yankin Arewa kamar aurar da ’yan mata da wuri, bakin talauci da rashin ilimi.

Wannan tsayuwar daka tasa ta sa wasu daga cikin manyan masu fada aji sun fara kallonsa a matsayin mai tada kura a cikin tsarin masarauta mai gargajiya.

Haka zalika, alakarsa da gwamnati, musamman da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ta kara tsananta, inda hakan ya kai ga rushe masarautar Kano ta hanyar kirkiro sababbi hudu domin rage masa karfi.

Wannan ya zama ginshikin sauke shi daga sarauta a watan Maris, 2020. Duk da haka, masoyansa da masu adawa da tsarin gargajiya na goyon bayan ra’ayinsa, suna kallonsa a matsayin jagoran sauyi.

Komawar Sanusi II kan karagar Kano a 2024 ta sake kunna wutar muhawara a Arewa, inda wasu ke kallon dawowarsa a matsayin nasara, yayin da wasu ke ganin hakan barazana ce ga zaman lafiya da daidaiton siyasar jihar.

An nemi diyya kan hana hawan sallah a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta yi korafi kan shafe shekaru ba tare da yin hawan sallah ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta biya ta diyya saboda hana hawan sallah a jihar.

Hakan na zuwa ne bayan hana gudanar da hawan da ake yi a jihar saboda rikicin masarautar da ake fama da shi bayan sauke Aminu Ado da Abba Kabir ya yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng