Ko Me Ya Yi Zafi: Kamfanin NNPCL Ya Rufe Matatar Port Harcourt
- Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya fitar da sanarwa ga ƴan Najeriya kan ayyukan matatar mai ta Port Harcourt da ke jihar Rivers
- Babban jam'in hulɗa da jama'a na kamfanin NNPCL ya sanar da cewa an rufe matatar domin gudanar da ayyukan da suka shafi yin gyare-gyare
- Femi Soneye ya bayyana cewa za a fara ayyukan gyaran ne a matatar daga ranar Asabar, 24 ga watan Mayun 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), ya sanar da rufe matatar mai ta Port Harcourt (PHRC) da ke jihar Rivers.
Kamfanin NNPCL ya sanar da cewa za a rufe matatar ta Port Harocurt ne domin gudanar da aikin gyara na musamman, wanda aka shirya farawa a ranar 24 ga Mayu, 2025.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin NNPCL, Femi Soneye, ya fitar a ranar Asabar, 24 ga watan Mayun 2205.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gyaran da za a yi wa matatar ta Port Harcourt an shirya fara shi ne a ranar 24 ga watan Mayun 2025, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Meyasa NNPCL ya rufe matatar Port Harcourt?
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa rufe matatar wani ɓangare ne na tsarin kulawa da tantance ɗorewar aiki domin tabbatar da ingantaccen aiki na matatar.
"Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) na sanar da jama’a za a rufe matatar Port Harcourt (PHRC) domin yin gyara na musamman da duba tsarin ɗorewar aiki."
"Wannan gyaran an shirya fara shi ne daga ranar 24 ga watan Mayu, 2025."
“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da duk masu ruwa da tsaki da suka haɗa da hukumar NMDPRA, domin tabbatar da cewa aikin gyaran da binciken ɗorewar aiki ya gudana cikin tsari da gaskiya."
"Kamfanin NNPCL na ci gaba da jajircewarsa wajen tabbatar da ɗorewar samar da makamashi mai ɗorewa da kariya ga ƙasar nan."
- Femi Soneye
Kamfanin ya ƙara da cewa za a ci gaba da samar da bayani a kai-a kai ta hanyoyin sadarwa na hukuma, ciki har da shafin yanar gizo, kafafen yaɗa labarai, da kuma fitar da sanarwa ga jama’a.

Asali: Twitter
Karanta wasu labaran kan kamfanin NNPCL
- Sabon shugaban NNPCL ya ci gaba da fatattaka, ya kori shugabannin matatun mai 3
- Dangote ya ziyarci NNPCL, za a gyara alakar da ta yi tsami a lokacin Kyari
- Mele Kyari: Tsohon shugaban kamfanin NNPCL ya fada komar hukumar EFCC
Kamfanin NNPCL ya rage farashin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya sauƙaƙawa mutanen Abuja ta hanyar rage farashin litar fetur.
Farashin da ake siyar da man fetur a gidajen mai na kamfanin NNPCL ya sauka daga kan N935 zuwa N910 kan kowace lita.
Wannan matakin da kamfanin ya ɗauka zai kawo sassauci ga direbobi da sauran masu amfani da man fetur wajen gudanar da harkinsu na yau da kullum.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng