Mele Kyari: Tsohon Shugaban NNPCL Ya Fada Komar Hukumar EFCC
- Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta ɗauko bincike kan yadda aka gudanar da kamfanin fetur na ƙasa (NNPCL)
- Binciken da hukumar EFCC ta fara ya jawo jami'an hukumar sun tsare tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari
- Majiyoyi sun bayyana cewa an tsare shi a ranar Juma'a, 2 ga watan Mayun 2025, kuma akwai yiwuwar zai yi kwanaki a hannun EFCC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, yana tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC).
Hakan na zuwa ne bayan hukumar EFCC ta fara bincike kan yadda aka tafiyar da kamfanin na NNPCL.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ce majiyoyi sun bayyana mata cewa ana tunanin Mele Kyari yana tsare a hannun hukumar EFCC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin fara bincikar Mele Kyari
Mele Kyari da wasu manyan jami'an kamfanin NNPCL da aka kora kwanan nan suna fuskantar bincike kan zargin almubazzaranci da kuɗaɗe da kuma amfani da ofishi ba bisa ƙa’ida ba.
An tsare Mele Kyari ne a ranar Juma'a, kuma akwai yiwuwar zai shafe kusan gaba ɗaya ranakun ƙarshen makon a hannun hukumar EFCC.
Jami'an hukumar EFCC sun yi tsit kan lamarin, duk da cewa wata wasiƙa tura ga sabon shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ta yi ta yawo a kafafen sada zumunta.
A cikin wasiƙar da EFCC ta aika, ta nemi a ba su takardu kan albashi da alawus-alawus na wasu manyan jami'ai 14, ciki har da waɗanda suka yi ritaya kuma ba sa aiki da kamfanin yanzu.
Sunayen jami’an da aka lissafo sun haɗa da, Abubakar Lawal Yar’Adua, Mustapha Magaji Sugungun, Mele Kolo Kyari, Kayode Olusegun Adetokunbo, Isiaka Abdulrazak, Efiok Michael Akp
Sauran su ne Umar Ajiya, Babatunde Bakare, Dikko Ahmed, Jimoh Olasunkanmi, Ibrahim Onoja, Bello Kankaya, Ademoye Adeniyi Jelli, da Desmond Inyama.

Asali: UGC
Bincike bayan sauye-sauye a NNPCL
Bayo Ojulari ya sauke daraktocin gudanarwa na matatun mai guda uku na Kaduna, Port Harcourt da Warri a cikin makon nan.
Kamfanin NNPCL a ƙarƙashin Mele Kyari ya kashe biliyoyin daloli wajen gyaran matatun mai, amma wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin sun bayyana cewa akwao sauran aiki kafin matatun su fara samar da abin da ake so.
Ƙungiya ta buƙaci a binciki Mele Kyari
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƙungiyoyin fararen hula sun buƙaci a binciki tsohon shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari.
Ƙungiyoyin sun buƙaci Mele Kyari ne kan yadda ya kashe kuɗaɗen da aka ware domin aikin gyaran matatar mai ta Port Harcourt da ke Rivers.
Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Michael Omoba, ya yaba da matakin da mai girma Shugaba Bola Tinubu na sauke Mele Kyari daga kan muƙaminsa.
Michael Omoba ya bayyana cewa yana kuma da kyau a binciki yadda aka tafiyar da kuɗaɗen da aka zuba domin gyaran matatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng