Dangote Ya Ziyarci NNPCL, Za a Gyara Alakar da Ta Yi Tsami a Lokacin Kyari

Dangote Ya Ziyarci NNPCL, Za a Gyara Alakar da Ta Yi Tsami a Lokacin Kyari

  • Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ziyarci sabon shugaban NNPCL Bashir Bayo Ojulari bayan sauke Mele Kyari
  • Kamfanin mai na kasar ya bayyana cewa an tattauna yadda za a ƙarfafa gasa mai kyau da tabbatar da tsaron makamashi a Najeriya
  • Yayin da NNPCL ya yaba da nasarorin Dangote, shugaban rukunin kamfanonin ya nuna gamsuwa da ƙwarewar sababbin shugabannin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya kai ziyara ga kamfanin mai na ƙasa wato NNPCL a ranar Laraba, 8 ga Mayu, 2024.

Ziyarar na iya zama wani yunkuri na dawo da dangantaka mai kyau tsakanin kamfanonin biyu bayan tangarɗar da aka samu a lokacin tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari.

NNPCL
Dangote ya kai ziyara kamfanin NNPCL na kasa Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

A cikin sakon da NNPCL ya wallafa a shafinsa na X, kamfanin ya bayyana cewa an tattauna ne kan yadda za a inganta haɗin gwiwa da zai amfanar da bangarorin biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da aka tattauna tsakanin NNPCL da Dangote

This day ta ruwaito cewa an kuma tattauna kan yadda za a ƙarfafa gasa mai tsafta a tsakanin kamfanonin biyu domin tabbatar da bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da jin daɗin al'umma.

A zamanin tsohon shugaban NNPCL, dangantakar kamfanonin biyu ta yi tsami musamman bayan matatar Dangote da ke Legas mai fitar da ganga 650,000 a rana ta fara sarrafa mai.

A lokacin, Dangote ya zargi NNPCL da gaza cika yarjejeniyar da ke tsakaninsu, wanda hakan ya matatar ta janye wani bangare na hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

NNPCL
Dangote ya tattauna da sabon shugaban NNPCL Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

Amma daga bisani NNPCL ya bayyana cewa jarin Dala biliyan ɗaya da ya saka ne ya taimaka wajen nasarar kammala matatar.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya musanta wannan ikirari, yana mai cewa zancen ba haka ya ke ba.

Za a gyara alakar NNPCL da matatar Dangote

A yayin wannan ziyarar, shugaban NNPCL na yanzu, Bashir Bayo Ojulari, ya yaba da nasarorin Dangote, yana mai bayyana shi a matsayin jagora abin koyi a nahiyar Afrika.

NNPCL ya ce:

“A safiyar yau, shugaban NNPC Ltd., Mr. Bashir Bayo Ojulari, ya karɓi baƙuncin tawagar kamfanin Dangote, wacce shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya jagoranta.”
“Mr. Dangote ya jaddada bukatar haɗin gwiwar da za ta canza abin da ake ganin ba zai yiwu ba zuwa abin da ya yiwu. Ya kuma yaba da tsarin sabon shugabancin NNPCL."

Ojulari ya ƙara da cewa tun lokacin da ya hau kujerar shugabanci, ya gano ƙwararrun ma’aikata a NNPCL waɗanda ke da himma da sadaukarwa don gina Najeriya.

NNPCL: Dangote ya magantu bayan sauke Kyari

A baya, mun wallafa cewa Attajirin Nahiyar Afrika kuma shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi magana kan sababbin shugabannin NNPCL bayan sallamar Mele Kyari.

Dangote ya yaba wa Bola Tinubu bisa zaben nagartattun shugabannin kamfanin mai na NNPCL bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa domin karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

Ziyarar ta nuna kyakkyawar alaka tsakanin Dangote da sababbin shugabannin NNPCL, wanda ke nuni da cewa za a inganta hadin gwiwa tsakanin kamfanonin biyu don cigaban Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.