Sauki Ya Kara Samuwa: Kamfanin NNPCL Ya Sauke Farashin Litar Man Fetur

Sauki Ya Kara Samuwa: Kamfanin NNPCL Ya Sauke Farashin Litar Man Fetur

  • Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya rage farashin litar man fetur daga N935 zuwa N910 a gidajen sayar da man sa da ke birnin tarayya Abuja
  • Rage farashin ya biyo bayan wata ganawa tsakanin shugaban NNPC da Aliko Dangote, suka amince da yin aiki tare domin kawo sassauci ga jama'a
  • Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa farashin fetur a gidajen man NNPCL da ke birnin Legas bai canza ba yayin da Dangote ya rage farashi a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Kamfanin man fetur na ƙasa, wato NNPCL ya dauki sabon mataki wajen rage farashin man fetur a Abuja.

Bayanai sun nuna cewa lamarin zai iya kawo ɗan sassauci ga direbobi da masu amfani da man fetur.

Gidan mai
NNPCL ya rage farashin man fetur a Abuja. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cewar rahoton da jaridar The Cable ta fitar ranar Talata, an lura da cewa farashin fetur a gidan man NNPC da ke Wuse Zone 3 ya sauka daga N935 zuwa N910.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauyin farashi na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye sauye a kasuwar man fetur, musamman bayan rage farashin man da Matatar Dangote ta yi zuwa N825 a ranar 12 ga Mayu.

Dangote da NNPC sun cimma matsaya

Bayan wata ganawa da suka yi a ranar 9 ga Mayu, shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, da shugaban Matatar Dangote, Aliko Dangote, sun bayyana aniyar yin aiki tare.

Shugaban NNPCL ya ƙara da cewa da zarar an samu sabon kaya a farashi mai sauki, za a rage farashin fetur a gidajen mai.

Ya bayyana cewa yawancin dillalan mai sun saye man yanzu a farashi mai tsada, shi ya sa farashin bai sauka ba gaba ɗaya.

Farashin fetur bai sauka a Legas ba

Ko da yake an samu sauyi a Abuja, farashin fetur a gidajen mai na NNPCL da ke Legas bai canza daga N935 ba, lamarin da ke nuna cewa canjin bai zama na ƙasa gaba ɗaya ba tukuna.

Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa ma ya nuna an samu saukin kudin litar man fetur a Abuja.

Ana fatan samun saukin fetur a Najeriya

Masu amfani da fetur, musamman direbobi da ‘yan kasuwa, sun nuna farin ciki da wannan mataki.

Wani mai aikin Keke Napep, Muhammad Adamu ya zantawa Legit cewa N25 da aka rage zai taimaka wajen saukaka wasu abubuwan.

Farashin mai
Masu aikin da abubuwan hawa sun nuna jin dadi da rage kudin mai. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Muhammad Adamu ya ce:

"Duk da cewa ragin kadan ne, idan mutum ya saye man da yawa zai ga saukin.
'Babban abin da ya kamata shi ne samun saukin a dukkan jihohi ba Abuja kawai ba."

Man fetur bai da tsayayyen farashi a Najeriya

Tun bayan fara mulkin shugaban kasa Bola Tinubu a Najeriya, farashin man fetur ya kasance yana tashi da sauka akai-akai, wanda hakan ya jawo damuwa da cece-kuce a tsakanin al’umma.

A lokuta da dama, gwamnati da kamfanonin mai na ƙasa kamar NNPCL suna ƙoƙarin daidaita farashin domin rage wa ‘yan kasa nauyi, amma canje-canjen farashin kasuwar duniya da sauran abubuwa sun yi tasiri.

A kwanan nan, kamfanin man fetur na ƙasa, NNPCL, ya rage farashin lita daga N935 zuwa N910 a Abuja, lamarin da ya zo bayan ganawar shugaban NNPC, Bayo Ojulari, da Aliko Dangote na matatar fetur.

Wannan sauyi ya kawo ɗan sassauci ga masu amfani da man fetur a babban birnin tarayya, amma a Legas farashin bai canza ba, wanda hakan ke nuna cewa canjin ba ya shafar ƙasar baki ɗaya.

Duk da haka, sauye-sauyen farashin man fetur a Najeriya na ci gaba da kasancewa wani babban ƙalubale ga tattalin arzikin ƙasa da rayuwar al’umma.

Masu amfani da mai suna fatan samun farashi mai sauƙi a ko’ina domin rage tsadar sufuri da kasuwanci.

Sai dai har yanzu rashin tabbas game da farashin fetur yana ci gaba da zama matsala a ƙarƙashin wannan sabon shugabanci.

Za a cigaba da hako mai a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta cigaba da hako mai a Arewa.

Baya ga haka, shugaban ya ce akwai aikin bututun gas da aka fara daga Ajakuta zuwa Kano da za a cigaba da shi.

A zamanin shugaba Muhammadu Buhari aka fara aikin hako man fetur a garin Kolmani da ke iyakar jihohin Gombe da Bauchi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng