Sabon Shugaban NNPCL Ya Cigaba da Fatattaka, Ya Kori Shugabannin Matatun Mai 3
- Sabon shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya cigaba da yin sauye-sauyen da suka janyo hankalin jama'a a fagen makamashi
- Wannan karon, Ojulari ya sauke shugabannin matatun man kasar nan guda uku da suka hada da ta Kaduna, Fatakwal da Warri don farfado da bangaren
- Rahoton ya ce babban burin hakan shi ne dakatar da ci gaba da salwantar darajar kadarorin tace mai a Najeriya wanda aka dade ana korafi a kai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kwanaki kadan bayan ya fara sauye-sauye, sabon shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya sake gudanar da wasu manya canje-canje.
Injiniya Ojulari ya sauke shugabannin matatun man kasar nan guda uku, Kaduna, Fatakwal da Warri, a wani yunƙuri na dakile ci gaba da salwantar da darajar kadarorin man Najeriya.

Asali: Facebook
The Cable ta wallafa cewa wannan gagarumin sauyi na da nufin dakatar da ci gaba da salwantar darajar sashen tace mai na Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan sauyi na zuwa ne a jim kadan bayan shugaban NNPCL, Injiniya Bayo Ojulari ya sauke wasu daga cikin manyan hukumar da aka ce suna da dangantaka da Mele Kyari.
NNPCL ya kashe kudi a kan matatun mai
This day ta ruwaito cewa NNPCL a karkashin Mele Kyari, ya kashe biliyoyin Daloli domin gyaran matatun amma majiyoyi daga cikin kamfanin har yanzu ba a samar da ci gaban da ake so ba.
Ojulari, wanda ya gaji Kyari kimanin makonni hudu da suka wuce, yana aiwatar da wani sabon tsari mai fadi domin tantance ainihin halin da matatun suke ciki.
Sabon shugaban ya kafa wani kwamiti, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kamfani mai kula da bangaren bangaren da ke kula da hada-hadar kayayyakin man fetur, Mumuni Dagazzau.

Asali: Facebook
Wannan kwamiti zai fara tattaki domin duba dukkannin matatun da NNPCL ke da su, tare da bayar da shawarwari bisa ainihin yanayin su.
Wata majiya ta bayyana cewa:
“Babban burin wannan sauyi shi ne dakatar da asarar darajar arzikin kasa da ake fuskanta a halin yanzu da kuma tsara yadda za a farfado da darajar matatun man kasa da bunkasa su don amfanin al'umma.”
Majiyar ta kara da cewa Ojulari zai ci gaba da daukar matakan farfado da NNPCL da ake zargin ta samu nakasu a zamanin Mele Kyari.
An kori manyan shugabanni a NNPCL
A wani labarin, mun wallafa cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) na ci gaba da yin garambawul a cikin gida tun bayan sauke tsohon shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari.
Sabon shugaban, Injiniya Bayo Ojulari, ya fara aiwatar da sauye-sauye da suka janyo sallamar manyan jami'ai da dama da aka fi dangantawa da tsohon shugaban, Mele Kyari a zamaninsa.
Daga cikin waɗanda aka cire daga muƙami akwai Bala Wunti, wanda ya kasance shugaban sashen zuba jari na NAPIMS, da kuma Ibrahim Onoja, Manajan Daraktan Matatar Man Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng