"Ba Zan Iya Ci Gaba da Zama ba," Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheƙa zuwa APC
- Jam'iyyar LP ta kara rasa ɗan Majalisar Wakilai daya daga jihar Enugu, ina Peter Obi ya nuna farin jininsa a babban zaben da ya wuce
- Mamba mai wakiltar mazaɓar Ezeagu/Udi a Enugu, Hon. Sunday Umahia ya tabbatar da sauya shekarsa daga LP zuwa APC a hukumance
- Sai dai wannan lamari bai yi wa shugaban marasa rinjaye daɗi ba, kuma ya tashi ya nuna adawa da yawan sauya jam'iyya a Majalisa ta 10
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan majalisar wakilai, Hon. Sunday Umehia, wanda ke wakiltar mazaɓar Ezeagu/Udi ta jihar Enugu, ya sanar da sauya shekarsa daga LP zuwa APC mai mulki.
Hon. Umehia ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa da ya mika wa kakakin Majalisar Wakilai, RT. Hon Tajudeen Abbas kuma ya karanta a zaman yau Alhamis.

Asali: Twitter
Me yasa ɗan Majalisar ya bar jam'iyyar LP
Ɗan Majalisar ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya raba LP gida uku ne ya tilasta masa barin jam'iyyar zuwa APC, kamar yadda The Nation ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba jam'iyyar LP ta dare gida uku; Tsagin Santa Nenadi Usman, Barista Julius Abure da na Lamidi Apapa, lamarin da ya jawo rashin tabbas game da shugabancin LP.
A wasiƙar da ya kai Majalisa don tabbatar da sauya shekarsa a hukumance, Hon. Sunday Umehia ya ce:
“Mun gaji da zaman rashin tabbas. Akwai shugabanni uku da ke ikirarin jagoranci, kuma mambobi da mabiya ba su san wanda za su bi ba."
Ya ce ya yanke shawarar shiga APC domin haɗa kai da Shugaban Ƙasa da jagororin jam’iyyar don kawo ci gaba a ƙasa nan, musamman yankin Kudu maso Gabas.
Ƴan adawa sun yi fatali da sauya sheƙar
Sai dai shugaban marasa rinjaye, Hon. Kingsley Chinda, ya soki wannan sauya sheƙa, yana mai cewa hakan na lalata darajar dimokuraɗiyya.
“Yawan sauya sheƙa da muke gani a Majalisa ya zama abin dariya ga tsarin mulkin dimokuraɗiyya.
Lokaci ya yi da za a sake nazari kan tanadin kundin tsarin mulki da ya shafi sauya jam’iyya,” in ji Chinda.

Asali: Facebook
'Ya kamata a kwace kujerun masu sauya sheka'
Ya buƙaci Kakakin Majalisar, Hon. Abbas Tajudeen, da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi domin ayyana kujerun masu sauya sheƙa a matsayin wadanda aka rasa.
Chinda ya kuma bayyana cewa hukuncin Kotun Ƙoli da ya warware rikicin shugabancin LP ya hana amfani da rikicin don sauya sheƙa.
“Kotun Ƙoli ta bayyana halastaccen shugaban LP. Don haka babu hujjar cewa rikicin cikin gida ya tilasta masa ficewa,” in ji shi.
Bugu da ƙari, Hon. Chida ya bukaci majalisar ta kwace shugabancin kwamitoci daga waɗanda suka bar jam’iyyarsu, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Sanata Lar ya fice daga LP zuwa APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan kwamitin kamfen Obi/Datti a 2023, Victor Lar ya jagoranci magoya bayansa sun koma APC a Filato.
Sanata Lar ya ce wannan mataki nasu na dawowa APC ba wai kawai shawara ce ta kashin kai ba, mataki ne da jama’a da dama suka yarda da shi.
A cewarsa, dama can shi ɗan APC ne wasu matsaloli ne suka sa ya barta gabannin 2023 amma yanzu an warware komai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng