Wata Mata, Zainab na Fuskantar Hukuncin Kisa saboda Ta Bar Musulunci a Zamfara? Gaskiya Ta Fito

Wata Mata, Zainab na Fuskantar Hukuncin Kisa saboda Ta Bar Musulunci a Zamfara? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin Zamfara karƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta karyata rade-raɗin maka wata Zainab a kotu kan sauya addini
  • Mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa labarin karyace da aka kirkira don tayar da zaune tsaye
  • Tun farko rahoton ƙaryar ya yi ikirarin cewa Zainab na fuskantar hukuncin kisa a jihar Zamfara saboda ta bar addinin musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gwamnatin Jihar Zamfara ta karyata rahoton da ke cewa wata mace mai suna Zainab na fuskantar shari'a a kotun Musulunci kan sauya addini.

Rahoton ya nuna cewa Zainab na fuskanta shari'a da kuma yiwuwar yanke mata hukuncin kisa, bayan ta fita daga musulunci ta koma kiristanci.

Gwamna Dauda Lawal.
Gwamnatin Zamfara ta musanta raɗe-raɗin cewa za a gurfanar da matar da ta bar addinin musulunci a gaban kotun shari'a Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Leadership ta ce a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar da daren Talata, ya bayyana cewa rahoton ƙarya ce tsagwaronta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce raɗe-raɗin ya samo asali ne daga shafukan sada sumunta kuma wasu masu neman jan hankali ne kawai suka ƙirƙire shi amma ba gaskiya ba ne.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati na tabbatarwa al'umma ba tare da shakka ba cewa babu irin wannan kara a gaban kowace kotun Shari’a a Jihar Zamfara.

Da gaske Zainab na fuskantar hukuncin kisa a Zamfara?

"Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu rahoton wani labarin karya da aka kirkira dangane da wata yarinya ‘yar shekara 22 mai suna Zainab Muhammadu, wadda aka ce tana fuskantar shari'a saboda sauya addininta zuwa Kiristanci.
“Muna sanar da cewa wannan labari aikin masu neman tayar da zaune tsaye ne, wadanda suke kokarin haddasa tashin hankali. Labarin bogi ne da wani shafin yanar gizo da aka sani da wallafa labaran karya ya yaɗa."
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauki matakin gaggawa ta hanyar kira da tantance gaskiyar lamarin daga hukumomi da jami’an tsaro, kuma an tabbatar cewa labarin karya ne daga shafin Sahara Reporters.

- Sulaiman Bala Idris.

Wane mataki gwamnatin Zamfara ta ɗauka?

Kakakin gwamna ya ƙara da cewa domin tabbatar da gaskiya, gwamnati ta tuntuɓi shugaban alƙalai na kotun shari'ar Musulunci na Zamfara.

“Don tabbatar da gaskiya, gwamnati ta tuntubi Babban Khadi na Kotun Shari’a ta Jihar Zamfara, kuma ya tabbatar babu irin wannan kara a gaban kowace kotun Shari’a a jihar.
“Tambaya ita ce, daga ina wannan rahoton da ya raba kan jama’a ya samo asali? Me masu yada shi suke son cimmawa?" in ji shi.
Dauda Lawal.
Gwamnatin Zamfara ta buƙaci hukumomin tsaro su kama masu hannu a yaɗa labaran Zainab Hoto: Dauda Lawal, Fr. Kelvin Ugwu
Asali: Facebook

Matar da ake yaɗa hotonta ba ƴar Najeriya ba ce

Bugu da ƙari, gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa hoton da ake yaɗawa na matar da ta koma kiristanci ba ƴar Najeriya ba ce, sunanta Aalia, kuma ƴar Texas ce a kasar Amurka.

A karshe, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su binciko asalin wannan labari na karya da ya yi nufin haddasa rikici na addini, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu.

Gwamnan jihar Zamfara ya kafe kan bakarsa

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal ya kafe kan matsayarsa cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ƴan bindiga ba.

Gwamna Dauda ya ce an samu ci gaba a fannin tsaro a jihar, amma har yanzu akwai wasu yankuna da ke buƙatar ɗaukin gaggawa.

Ya ƙara da cewa babu maganar sulhu a Zamafara amma waɗanda suka miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba, ana karɓarsu cikin lumana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262