Gwamnoni 36 Sun Yi Rashin Nasara, Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Kuɗin da Aka Ƙwato daga 'Ɓarayi'

Gwamnoni 36 Sun Yi Rashin Nasara, Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Kuɗin da Aka Ƙwato daga 'Ɓarayi'

  • Gwamnonin Najeriya sun yi rashin nasara a karar da suka ƙalubalanci gwamnatin tarayya kan kuɗin da aka kwato daga hannun ɓarayi
  • Kotun ƙolin ta yi watsi da karar yau Juma'a, ta ce kamata ya yi gwamnoni su shigar da ƙorafinsu a babbar kotun tarayya
  • Tun farko, gwamnonin sun soki yadda gwamnatin tarayya ta kashe kuɗin ita kaɗai, ba tare da kasafta su da jihohi da ƙananan hukumomi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kotun Koli ta yi watsi da karar da gwamnonin jihohi 36 da Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) suka shigar kan kudin da aka ƙwato daga ɓarayin gwamnati.

Gwamnonin sun kalubalanci yadda Gwamnatin Tarayya ke amfani da kudaden da aka karbo daga wuraren da aka yi almundahana da dukiyar kasa ba tare da bin ƙa'ida ba.

Kotun koli.
Kotun Koli ta yi fatali da ƙarar da gwamnoni suka shigar kan kudin da aka kwato Hoto: Supreme Court
Asali: Facebook

Kotun koli ta kori ƙarar gwamnoni 36

Kwamitin alƙalai bakwai ne ya yanke wannan hukunci a zaman kotu na yau Juma'a, 23 ga watan Mayu, 2025, kamar yadda The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hukuncin wanda mai shari'a Chidiebere Uwa ta rubuta kuma mai shari'a Mohammed Idris ya karanta, kotun ta ce masu kara sun shigar ƙarar a wurin da bai dace ba.

Kotun ta bayyana cewa lamarin ya fi dace wa a saurare shi a Babbar Kotun Tarayya, ba a Kotun Koli ba.

Gwamnonin jihohin sun zargi Gwamnatin Tarayya da rashin bin ƙa'idar kundin tsarin mulki wajen raba kudaden da aka karbo daga ɓarayi tsakanin 2015 da 2021.

Wane kuɗi gwamnoni suka kai kara a kansu?

Sun ce kudaden da aka dawo da su sun hada da:

  • ₦1.8tr na kudi
  • Gidaje 167
  • Motoci 450
  • Manyan motocin dakon kaya 300
  • Gangar danyen mai miliyan 20 (kimanin Naira biliyan 450).

Gwamnoni 36 sun ƙalubalanci gwannatin tarayya

Sun ce maimakon a tura kudaden zuwa Asusun Tarayya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, Gwamnatin Tarayya tana karkatar da su zuwa lalitarta.

Gwamnonin jihohin sun kara da cewa buɗe wasu sababbin asusu kamar asusun tara kuɗin almundahana da aka kwato ya saɓawa tanadin doka, Vanguard ta rahoto.

Gwamnoni.
Kotun koli ta ce ba ta da hurumin sauraron karar da gwamnoni suka hsigar gabanta kan kuɗaɗen da aka kwato daga hannun ɓarayi Hoto: @NGFSecretariat
Asali: Facebook

Sun dogara da sashe na 162(1), 162(10), da 80 na kundin tsarin mulki, da kuma dokar kuɗi, 1958, don jaddada cewa kudaden da aka karbo sun zama kamar kuɗin shiga da ake kasaftawa tsakanin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Daga karshe, sun bukaci kotun ta tilasta ma Gwamnatin Tarayya ta mayar da ₦1.8tr da kuma karin ₦450bn na kadarorin da aka kwace zuwa Asusun Tarayya.

Sai dai Kotun Koli ta ce karar ba ta cikin huruminta ba kuma kamata ya yi a shigar da ita a Babbar Kotun Tarayya, don haka ta yi watsi da ita gaba daya.

Gwamnatin Tarayya za ta yi gwanjon gidaje

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta shirya gwanjon gidaje 753 da aka ƙwato daga hannun Godwin Emefiele.

Tuni dai hukumar EFCC ta mika gidajen, da ke cikin yankin Cadastral na birnin tarayya Abuja, ga ma’aikatar gidaje da ci gaban birane ta Najeriya.

Ministan gudaje, Ahmed Musa Dangiwa, ya tabbatar da cewa za a bi tsarin da ya dace cikin gaskiya da adalci wajen sayar mutane waɗannan gidaje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262