An Gano yadda aka Sace Hamdiyya a Sokoto, Aka Tsira Mata Allura a Daji
- Dakarun tsaro sun ceto budurwar nan ’yar shekara 19, Hamdiyya Sidi Sharif daga hannun miyagu masu garkuwa a Bakura, Jihar Zamfara
- An gano Hamdiyya ne yayin sintiri a dajin da ke kan hanyar Lambar Bakura – Yar Geda a karamar hukumar Bakura a ranar 21 ga Mayu, 2025
- An garzaya da ita asibiti domin duba lafiyarta bayan nan kuma jami’an tsaro sun tafi da ita ofis domin ci gaba da kula da ita a karkashinsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - A wani samame da jami’an tsaro suka gudanar a dazukan karamar hukumar Bakura da ke Jihar Zamfara, an samu nasarar ceto Hamdiyya Sidi Sharif.
Wannan nasara ta zo ne a ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, yayin wani sintiri da jami’an tsaro ke yi a dajin da ke kan hanyar Lambar Bakura zuwa Yar Geda.

Asali: Facebook
Rahoton da mai bincike kan sha’anin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X ya bayyana cewa Hamdiyya na daga cikin masu rajin yaki da rashin tsaro a jihar Sokoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ceto Hamdiyya a dajin Zamfara
Wani jami’in ’yan sanda ya shaida cewa an ceto Hamdiyya ne da misalin karfe 1:00 na rana a cikin daji.
Bayan ganinta, an garzaya da ita zuwa asibiti domin duba lafiyarta, kuma rahotanni sun nuna cewa tana samun sauki sosai.
Dama dai masu garkuwa da mutane sun addabi yankin Bakura da kewaye, lamarin da ya tilasta hukumomi kara tsaurara matakan tsaro ta hanyar sintiri don shawo kan barazanar.
An yi wa Hamdiyya allura a daji
Wani bidiyo da Mai Biredi TV ya wallafa a Facebook ya nuna cewa jami'an asibitin sun bukaci 'yan sanda su tafi da ita caji ofis bayan ta fara samun sauki.
Wani daga aka yi hira da shi a bidiyon ya ce babu abin da ya samu lafiyarta a zahiri, sai dai ta ce mutanen da suka sace ta sun mata allura a hannunta.
Bayan an tsira mata allurar ne ciwon kai ya kamata a dajin kafin a yi nasarar ceto ta.
Yadda aka sace Hamdiyya a Sokoto
A kwanakin baya, Hamdiyya ta bayyana damuwa kan yadda al’umma ke zama ’yan gudun hijira a cikin jiharsu.
Sai dai a ranar Laraba aka ji labarin cewa an sace Hamdiyya yayin da ta je kasuwa sayo kayan abinci.

Asali: Facebook
Ta bayyana cewa tana dawowa gida ne wasu mutane sanye da kayan 'yan sanda suka tare ta a kan abin hawa.
Hamdiyya ta bayyana cewa nan take fara mata tambayoyi kuma daga nan ne hankalinta ya bace sai daga karshe ta samu kanta a cikin daji.
Amnesty ta yi magana kan batar Hamdiyya
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Amnesty ta yi magana bayan bacewar Hamdiyya a jihar Sokoto.
Amnesty International ta ce bai kamata a rika neman masu fadawa gwamnati gaskiya kan tsaro ana rasawa ba.
Hakan na zuwa ne bayan 'yan Najeriya na magana kan sanarwar da ta fito cewa ba a ga matashiyar ba ana kokarin kammala shari'arta a Sokoto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng