A Ƙarshe, An Gano Hamdiyya a Zamfara, An Faɗi Halin da Take Ciki
- An gano Hamdiyya Sidi Sharif a babban asibitin Bakura da ke Zamfara cikin mawuyacin hali, bayan ta ba ce ranar Talata a Sokoto
- Lauyanta, Abba Hikima, ya ce an sace ta ne a Sokoto lokacin da ta fita sayo kayan miya, kuma yanzu haka jami'an tsaro na tare da ita
- Amnesty International ta nemi a gudanar gaggawar bincike kan batan matashiyar yayin da ta yi zargin cewa ana yunkurin rufe bakinta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara — An gano Hamdiyya Sidi Sharif, matashiya mai fafutukar kare hakkin jama’a kuma babbar mai sukar gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, bayan awanni da bacewar ta.
Abba Hikima, lauyan matashiyar ya ce an gano Hamdiyya a cikin mawuyacin hali, inda yanzu take kwance a babban asibitin gwamnati na Bakura da ke jihar Zamfara.

Asali: Facebook
Hamdiyya na cikin mawuyacin hali a Zamfara
A sanarwar da Abba Hikima ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 15 ga Mayu, 2025, ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An shaida mana cewa Hamdiyya na babban asibitin gwamnati na Bakura, jihar Zamfara. Tana cikin mawuyacin hali, amma tana tare da jami’an tsaro.”
Hikima ya kuma tabbatar da cewa an sace Hamdiyya ne a jihar Sokoto kafin daga bisani kuma aka gano ta a asibitin na Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa ta ɓace ne tun ranar Talata bayan ta gaza dawowa gida, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a tare da haifar da faɗaɗɗen kamfen a yanar gizo na neman bayani kan inda take.
Amnesty ta nemi a binciki batan Hamdiyya
A sa’o’i kaɗan bayan ɓacewar Hamdiyya, kungiyar Amnesty International reshen Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook cewa:
“Amnesty International na cike da damuwa kan ɓacewar Hamdiyya Sidi Sharif wadda gwamnatin Sokoto ta gurfanar da ita bisa zargin amfani da kalmomin batanci da tunzura jama’a, saboda sukar Gwamna Ahmed Aliyu.
“Dole ne hukumomin Najeriya su gaggauta bincike don gano hakikanin abin da ya faru da kuma inda Hamdiyya take.”
Zargin da gwamnatin Sokoto ke yi wa Hamdiyya
Hamdiyya mai shekaru 18 ta fuskanci ƙalubale masu yawa a kotu cikin watannin baya, sakamakon sukar yadda Gwamna Ahmed Aliyu ke tafiyar da harkokin tsaro a jihar Sokoto.
A baya an gurfanar da ita bisa zargin tunzura jama'a da amfani da kalmomin batanci, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasa baki ɗaya.
Kungiyar Amnesty International ta soki yadda ake tafiyar da lamarin Hamdiyya Sahrif, inda ta kira hakan da cin zarafin ’yancin faɗar albarkacin baki a Najeriya.
Haka nan kungiyar ta nemi a tabbatar da an kare Hamdiyya da lauyanta, tare da neman hukumomi da su binciki barazana da matsin lambar da suke fuskanta.

Asali: Facebook
A watan Nuwamba 2024, rahotanni sun bayyana cewa an sace Hamdiyya, aka lakada mata duka tare da barin ta da raunika masu muni.
Ci gaba da kai ma Hamdiyya hari ya haifar da fushi daga matasa da kungiyoyin farar hula da ke ganin hakan wani yunkuri ne na rufe bakinta da tsoratar da masu adawa.
Babu sanarwa daga gwamnatocin Zamfara, Sokoto
Har zuwa daren yau Laraba, babu wata sanarwa daga gwamnatocin Sokoto ko Zamfara game da yanayin da Hamdiyya take ciki ko yadda ta tsinci kanta a Bakura.
Lauyanta da magoya bayanta suna ci gaba da kira da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, domin tabbatar da gaskiya da hukunta masu hannu a lamarin.
Amnesty ta soki gwamnati kan Hamdiyya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, kungiyar Amnesty International ta zargi gwamnatin jihar Sokoto da yunƙurin hana yancin gwagwarmaya da fadar gaskiya a fadin jihar.
Wannan zargi na zuwa ne bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun sace yar gwagwarmaya Hamdiyya Sidi Sharif tare da lakada mata dukan kawo wuka.
Amnesty International ta ce bai kamata gwamnatin Sokoto ta yi ƙoƙarin rufe bakin waɗanda ke bayyana halin kunci da rashin tsaro da al’umma ke ciki ba.
Asali: Legit.ng