Tirkashi: Kasar Iran Ta Gindaya Sharadin Cimma Yarjejeniya da Amurka
- Ana ci gaba da zaman jira domin ganin an cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran kan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
- Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa akwai sharadin da sai an cika shi kafin a kulla wata yarjejeniya da kasar Amurka
- Hakazalika, Iran ta zargi Amurka da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a tsakanin bangarorin biyu a watan Afrilun 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Iran ta yi magana kan kulla yarjejeniya da Amurka.
Ma'aikatar harkokin wajen ta bayyana cewa tsagaita bude wuta a ƙasar Lebanon ya kasance babban sharaɗi ga kowace irin yarjejeniya da Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin Gabas Ta Tsakiya.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen, Esmaeil Baqaei, ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai na mako-mako a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.
Wane sharadi Iran ta kafa?
“Muna jaddada cewa tsagaita bude wuta a Lebanon muhimmin sharaɗi ne ga kowace yarjejeniya da ke da nufin kawo ƙarshen yaƙin."
- Esmaeil Baqaei
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi alƙawarin tsananta kutse a cikin Lebanon, kuma kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ta shirya gudanar da taron gaggawa a ranar Litinin bayan da sojojin Isra'ila suka karɓi ikon tsohon babban gidan sarauta na Beaufort castle.
Baqaei ya ce Iran za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tallafa wa Lebanon da kuma dakarun gwagwarmaya muddin ana fuskantar haramtaccen farmakin gwamnatin Israila.
Iran ta yi zargi kan Amurka
Haka zalika, babban mai tattaunawa na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya soki katsewar zirga-zirga ta hanyar ruwa da dakarun sojan ruwan Amurka suka yi wa tashoshin jiragen ruwan Iran tun daga ranar 13 ga watan Afrilu.
Ghalibaf a wani rubutu a shafinsa na X ya ce toshe tashoshin jiragen ruwan da tsanantar faɗa a Lebanon sun kasance “shaidu a sarari na rashin bin ƙa'idar tsagaita bude wuta da Amurka ta yi.”
“Kowane zaɓi yana da farashi, kuma lokacin biyan lissafin kuɗin ya yi."
- Mohammed Bagher Ghalibaf

Source: Getty Images
Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka, Iran
Wannan furuci yana zuwa ne a daidai lokacin da Tehran da Washington ke ci gaba da musayar saƙonni a ƙoƙarin kammala tsarin yarjejeniya da ke da nufin kawo ƙarshen yaƙin.
Yakin dai ya ɓarke ne sakamakon hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila a kan Iran a ƙarshen watan Fabrairu, wanda kuma daga baya ya mamaye yankin baki ɗaya.
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Iran, Amurka, da Isra'ila ta kasance tana aiki tun ranar 8 ga watan Afrilu, amma rikici na ci gaba a Lebanon duk da jaddadawar da Tehran ta yi na cewa ya kamata yarjejeniyar tsagaita bude wutan ta shafi ƙasar Lebanon.
Harin Iran ya jikkata jami'an Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta kai wani harin ramuwar gayya kan sansanin sojojin Amurka da ke kasar Kuwait.
Sojojin Amurka huɗu tare da wasu ma’aikatan kwangila uku ne suka samu raunuka sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai.
An samu tabbacin cewa harin bai yi wata gagarumar illa ba, domin dukkanin jami'an da ma'aikatan kananan raunuka kawai suka samu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

