Ana Tunanin Haɗaka a ADC, Atiku Abubakar Ya Jefa Magoya Bayan PDP a Duhu

Ana Tunanin Haɗaka a ADC, Atiku Abubakar Ya Jefa Magoya Bayan PDP a Duhu

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba shi da niyyar fita daga cikin jam'iyyarsa ta PDP yayin da ake batun hadakar adawa
  • Atiku na daga cikin tattaunawa da wasu manyan ’yan adawa kamar Peter Obi da Nasir El-Rufa'i domin hada karfi wajen tunkarar APC kafin zaben 2027
  • Daga cikin abubuwan da hadakar ke dubawa akwai yiwuwar kafa sabuwar jam'iyya ko a yi amfani da wasu jam'iyyun adawa da ake da su a yanzu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga PDP domin shiga sabuwar hadakar adawa da ake kokarin kafa wa.

Wannan karin haske ya fito daga bakin hadiminsa na yada labarai, Paul Ibe, wanda ya bayyana cewa Atiku na ci gaba da tattaunawa da wasu fitattun 'yan adawa kan hadakar.

Atiku
Atiku ya karyata shirin ficewa daga PDP Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television inda ya ce ana tattaunawa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da Peter Obi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar na tattaunawa da Nasir El-Rufa’i

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Paul Ibe ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa dangane da kafa hadakar adawa mai karfi kafin zaben 2027.

Ya ce:

“Shugaba na ya fada cewa ba zai bar PDP ba kuma ya kamata a girmama wannan matsayi nasa. Babu bukatar in zo nan in yi karin bayani a kai. Ya riga ya yi magana a kai."
“Akwai wata tattaunawa da ke gudana tsakanin Atiku Abubakar da wasu manyan ’yan adawa kamar su Peter Obi da Nasir El-Rufai. Eh, hakan gaskiya ne. Ana kan tattaunawa. Bayan kammala wannan tattaunawa, za su fitar da matsayi da kuma hanyar da za a bi dangane da bukatu da fatun ‘yan Najeriya.”

Yadda gwamnonin PDP ke kallon hadakar adawa

Duk da kasancewarsa jigo a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na tattaunawa da wasu jiga-jigan 'yan adawa a kan hadakar jam’iyyu kafin 2027.

Atiku
Atiku Abubakar ya ce yana nan a cikin PDP Hoton: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sai dai gwamnonin PDP tuni sun bayyana matsayarsu dangane da hadakar adawa, inda suka bayyana cewa ba za su shiga kawance ko hadaka da kowace jam’iyyar adawa ba.

A martani ga wannan batu, daya daga cikin jiga-jigan hadakar kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana dama babu PDP a lissafinsu.

Ya ce tuntuni suka gano cewa akwai babbar matsala a tattare da PDP wacce kuma zai yi wahala a cimma matsaya wajen warware ta.

Hadakar adawa ta karyata zaben ADC

A baya, mun wallafa cewa hadakar adawa ta nesanta kanta daga rahotannin da ke cewa ta amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da za ta yi amfani da shi a 2027.

Wani jigo a cikin hadakar da ya yi magana a madadinta, Salihu Moh. Lukman, ya fadi hakan a cikin sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga Mayu, a Abuja.

A cewarsa, labarin da ke yawo cewa an zabi ADC ko cewa an nada shi a matsayin shugaban ofishin hadakar siyasar karya ne da ake son amfani da shi domin raba kawunansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.