"Gwamnoni ba Za Su Yarda a Rushe Hukumomin Zaben Jihohi ba," Gwamna Sule Ya Kawo Mafita

"Gwamnoni ba Za Su Yarda a Rushe Hukumomin Zaben Jihohi ba," Gwamna Sule Ya Kawo Mafita

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa gwamnoni ba za su amince a rushe hukumomin zaɓen jihohi ba
  • Sule ya ce rushe hukomomin ba shi ne zai warware matsalolin da suke fuskanta ba saboda ita kanta INEC tana da nata ƙalubalen
  • Gwamnan ya ce kamata ya yi a zauna a gyara hukumomin domin inganta ayyukansu maimakon rushe su gaba daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa gwamnoni ba za su goyi bayan soke hukumomin zaɓe na jihohi (SIECs) ba.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce kamata ya yi a yi wa hukumomin zaɓen jihohin garambawul domin ƙara inganta su maimakon a ce za a rushe su gaba ɗaya.

Gwamna Sule.
Gwamnoni ba za su yarda a soke hukumomin zaben jihohi ba Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Asali: Twitter

Sule ya bayyana haka ne da yake jawabi a wurin taron deleget na kungiyar hukumomin zaɓe masu zaman kansu (FOSIECON) karo na 13 a Jos, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni ba za su yarda a rushe SIECs ba

Gwamna Sule ya ce kiran da ake yi na a soke SIECs ba abu ne mai kyau ba, domin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa watau INEC na fuskantar irin matsalolin da na jihohi ke fama da su.

“Na yarda 100 bisa 100 cewa soke SIECs ba mafita ba ce, kuma ba za mu goyi bayan hakan ba.
"Matsalolin da hukumomin zaɓen jihohi suke fuskanta, wato katsalandan daga ‘yan siyasa da rashin isasshen kudi, har a matakin ƙasa (INEC) ana fama da su."

- Abdullahi Sule.

Ƙalubalen da hukumomin zabe ke fuskanta

Ya ce manyan matsalolin da ke hana SIECs aiki yadda ya kamata sun hada da matsin lamba daga gwamnatin jiha, karancin kudade, da rashin amincewar jama'a.

“A cikin shekaru shida da na yi a matsayin gwamna, na ga cewa katsalandan da rashin kudi sune manyan kalubale da ke hana wadannan hukumomi yin aikin su yadda ya kamata,” in ji shi.

Gwamna Sule.
Abdullahi Sule ya lissafa kalubalen da hukumomin zaɓen jihohi ke fuskanta Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Asali: Facebook

Gwamna Sule ya bayyana cewa masu kwaɗayin mulki da muƙamin siyasa ne suke neman a soke hukumomin zaɓen jihohi don cika burinsu amma ba don gyara ba.

“Bai danganci ci gaban dimokuraɗiyya ba, abu ne da ya shafi kwaɗayin mulki. Muna bukatar shugabanni masu hangen nesa da rikon amana,” in ji gwamnan.

Ya kuma bayyana cewa yawancin gwamnoni za su goyi bayan duk wata mafita ko shawarwari da za su fito daga taron domin farfado da ayyukan SIECs, rahoton Punch.

FOSIECON ta nemi a mutunta doka

A bangarensa, Shugaban FOSIECON, Jossy Chibunde Eze, ya bukaci a mutunta kundin tsarin mulki tare da baiwa SIECs 'yanci da cin gashin kansu na kudi.

Ya kuma koka kan yadda gwamnoni ke amfani da ikon su wajen kawo cikas ga ayyukan hukumomin zaɓen jihohi.

“SIECs na da ikon cin gashin kansu a dokar kasa, amma saboda dogaro da gwamnoni wajen kudade, su kan fuskanci matsin lamba,” in ji Eze.

Gwamna Sule zai fito takarar sanata a 2027?

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa zai nemi takarar sanata a 2027.

Gwamna Sule ya ƙarya raɗe-raɗin, yana mai bayyana su a matsayin ƙanzon kurege da ba su da tushe ballantana makama.

Ya ce duk da kiraye-kirayen da ake yi masa, ba shi da sha'awar tafiya Majalisar Dattawa a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262