Gwamna Ya Fara Tunanin Rayuwa bayan Barin Mulki, Ya Fadi Sana'ar da zai Koma
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya fara tunanin sana'ar da zai koma bayan ya kammala wa'adin mulkinsa a shekarar 2027
- Abdullahi Sule wanda ya ce shi ƙwararren mai walda ne, zai koma sana'arsa ta asali bayan ya sauka daga kan mulki
- Gwamnan ya kuma bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen jawo masu zuba hannun jari zuwa jihar Nasarawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan sana'ar da zai koma bayan ya kammala wa'adin mulkinsa.
Gwamna Sule ya bayyana shirinsa na komawa sana’ar da ya fara da ita ta asali wato aikin walda, da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2027.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta ce Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wani taron tattaunawa da hukumar samar da wutar lantarki ta karkara (REA) ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi amfani da damar wajen tabbatarwa da masu sha'awar zuba jari cewa jihar Nasarawa na da ƙwararrun ma'aikata, ya nuna cewa jihar na da ɗimbin matasa masu horo da shaidar ƙwarewa da za su iya tallafawa masana’antu.
Wace sana'a Gwamna Sule zai koma?
"Ɗaya daga cikin abubuwa da suka fi burge ni shi ne, na fara karatuna a matsayin masani a fannin fasaha, ina aikin walda, kafin na koma CNC da sauran su."
"Kamar yadda kuke ganina, na ƙware a fannin walda, da zarar na kammala gwamna, zan koma aikin walda. Saboda haka ne muka yanke shawarar sanya koyon sana’o’i a jihar Nasarawa ya zama abin alfahari."
“Muna da ɗaya daga cikin cibiyoyin koyon sana’o’i mafi inganci a bisa ƙa’idar NBTE. A gaskiya, yawancin manyan kamfanoni da ke horar da ma'aikatansu har ma da waɗanda kenan Abuja, suna zuwa su yi horo a wannan cibiyar da ke Nasarawa."
"Babban burinmu shi ne, duk kamfanonin da ke zuwa, mu samar musu da ƙwararrun masu fasaha da za su yi aiki a cikinsu."
- Gwamna Abdullahi Sule

Asali: Facebook
Nasarawa na jawo hankalin masu zuba jari
Gwamnan ya kuma bayyana matakan da gwamnatinsa ta ɗauka domin jawo hankalin masu zuba jari zuwa jihar Nasarawa.
"Yawancin abubuwan da muke yi domin kare zuba jari a Nasarawa ana yin su ne bisa doka. Mun gabatar da ƙudurori daga ɓangaren zartarwa domin kare zuba jari. Mun yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar."
"Idan kana neman masu zuba jari kuma ka san yadda ake neman su, to dole ne ka yi aiki tukuru wajen samar da zaman lafiya. Saboda kowane mai zuba jari yana son ya tabbatar da tsaro kafin komai."
- Gwamna Abdullahi Sule
Me gwamnoni ke samu bayan baris ofis?
A Najeriya, yawancin gwamnonin da suka gama wa’adinsu na ci gaba da samun kuɗi daga gwamnati ta hanyoyi daban-daban.
Da farko, dokokin da wasu majalisun dokoki na jihohi suka kafa na bai wa tsofaffin gwamnonin fansho wanda ya haɗa da albashi na kowane wata, gidaje, motoci da masu gadi.
A ciki har da tikitin jirgi na kasashen waje da na cikin gida, da kuma kula da lafiyarsu da iyalansu.
Wannan ya sa yawancin gwamnonin da suka sauka daga mulki ba sa komawa sana’ar da suka fito daga ita.
Har ila yau, wasu daga cikinsu kan samu mukamai daga gwamnatin tarayya ko a cikin jam’iyyunsu na siyasa, wanda hakan ke ci gaba da ba su damar samun kudi da tasiri.
Wasu kuma na shiga harkokin kasuwanci da kwangiloli, inda suke amfani da tasirin da suka samu a lokacin mulki.
Saboda haka, bayan mulki, rayuwar yawancin gwamnonin Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin jin daɗi.
Amma kalaman Gwamna Abdullahi Sule na cewa zai koma sana’ar walda bayan ya sauka, ya saba da al’adar da aka saba gani a kasar; inda yawanci ke ci gaba da rayuwa cikin alfarma da jingina da dukiyar jama’a.
Nasarorin Tinubu ke sa a shiga APC - Sule
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya taɓo batun komawa jam'iyyar APC da ƴan adawa ke yi.
Gwamna Sule ya bayyana cewa nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ne suka sanya ƴan adawa ke yin tururuwa zuwa APC.
Ya nuna cewa jam'iyyar APC na da burin ganin ta samu rinjayen da zai sanya ta riƙa lashe mafi yawan ƙuri'u a lokacin zaɓe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng