Gwamnan Nasarawa Ya Yi Bayani kan Batun Yin Takara a Zaben 2027

Gwamnan Nasarawa Ya Yi Bayani kan Batun Yin Takara a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya fito ya yi magana kan batun cewa zai yi takatar kujerar sanata a zaɓen 2027
  • Abdullahi Sule ya musanta rahotannin da ke cewa bayan ya gama gwamna a Nasarawa zai nemi tafiya majalisar dattawa
  • Gwmanan ya bayyana cewa abin da ya fi maida hankali a kai a yanzu shi ne sauke nauyin da ke kansa na al'ummar jihar Nasarawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa zai tsaya takarar Sanata a zaɓen 2027.

Gwamna Sule ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa a zaɓen shekarar 2027.

Abdullahi Sule
Gwamna Sule ya musanta batun yin takara a 2027 Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Ibrahim Addra, ya fitar a ranar Talata, 21 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana rahotannin da ke yawo a kai a matsayin na ƙarya, masu cike da ruɗani kuma marasa tushe.

Wannan ƙaryatawar ta biyo bayan wata magana da Suleiman Musa-Nagogo, darakta-janar na hukumar kula da fanshon jihar, ya yi yayin wani taro da jiga-jigan jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Wamba.

Musa-Nagogo ya yi iƙirarin cewa gwamnan ya shaida masa cewa yana da niyyar tsayawa takarar Sanata.

Me Gwamna Sule ya ce kan takarar Sanata?

Sai dai, a cikin sanarwar da sakataren watsa labaran gwamnan ya fitar, ya musanta wannan iƙirarin, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

"Wannan magana ba gaskiya ba ce, kuma ba ta fito daga Gwamna Abdullahi Sule ba. Gwamna bai taɓa ganawa da kowanne mutum ko ƙungiya domin bayyana ko tallata wata takara ta siyasa ba, ciki har da takarar Sanata."

- Ibrahim Addra

Ya bayyana cewa gwamnan ya karɓi kiraye-kiraye daga mutane da ƙungiyoyin siyasa daban-daban da ke roƙonsa ya tsaya takarar Sanata.

Jami'in ya jaddada cewa Gwamna Sule koyaushe yana ƙin amincewa da irin waɗannan kiraye-kirayen.

“A dukkan irin waɗannan lokuta, Gwamna Sule ya bayyana a fili cewa hankalinsa na kan cika alkawuran da ya ɗauka lokacin da aka zaɓe shi gwamna, da kuma tabbatar da ci gaban jihar Nasarawa."

- Ibrahim Addra

Abdullahi Sule
Gwamna Sule bai da ra'ayin yin takara a 2027 Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Twitter

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan na ci gaba da jajircewa wajen kyautata mulki da kuma barin jihar a wuri mafi kyau fiye da yadda ya karɓe ta.

Duk da godiya ga irin goyon baya da yabo da yake samu daga abokai da abokan siyasa, ya sake jaddada cewa bai bayyana wata sha’awa ta tsayawa takara a kowacce kujera ta siyasa ba a nan gaba.

Gwamna Sule ya faɗi sana'ar da zai koma

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan sana'ar da zai koma bayan ya sauka daga mulki.

Gwamna Sule ya bayyana cewa yana da shirin komawa sana'arsa ta asali wato walda idan ya yi sallama da mulki a watan Mayun shekarar 2027.

Ya nuna cewa gwamnatinsa ta samar da wuraren koyar da sana'o'i masu yawa a jihar Nasarawa domin matasa su dogara da kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng