PDP ko SDP? Babachir Lawal Ya Faɗi Shirinsu kan Jam'iyyar da Za a Yi Haɗaka kafin 2027
- Babachir Lawal ya ce ba zai yiwu ƴan adawa su yi amfani da PDP a matsayin jam'iyyar haɗaka ba saboda tana fama cuta mara magani
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya buƙaci ƴan Najeriya su kwantar da hankulansu domin nan ba da jimawa ba za a gama shirye-shiryen haɗaka
- Babachir ya ce Atiku Abubakar na da ƴancin neman takara amma ba zai yanke hukuncin a wace jam'iyyar zai nemi hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya yi fatali da yiwuwar ƴan adawa su yi amfani da PDP a matsayin jam'iyyar haɗaka a 2027.
Babachir Lawal ya ce ba zai yiwu a yi amfani da babbar jam'iyyar adawa watau PDP ba saboda tana fama da cutar da ba a san maganinta ba.

Asali: Twitter
Tsohon SGF ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin The Morning Show na Arise News TV a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wace jam'iyya jagororin adawa za su yi haɗaka?
A rahoton da Leadership ta tattaro, Babachir ya ce:
“Mun kusa da kammala shirye-shiryen, kuma ba da jimawa ba za mu bayyana jam’iyyar da za ta jagoranci haɗakar ko mu yi rajistar sabuwar jam’iyya.
"Yan Najeriya suna cikin damuwa na rashin sanin halin da ake ciki, don haka mun hanzarta shirin domin rage zama cikin duhu a tsakaninmu.”
PDP za ta iya zama jam'iyyar haɗaka?
A lokacin da aka tambaye shi ko PDP za ta iya zama da za su yi amfani da ita, Babachir Lawal ya musanta hakan.
“A duka nazarin da muka yi zuwa yanzu, babu wanda ya ambaci PDP a matsayin dandalin da za a yi amfani da shi.
"Mun amince gaba daya cewa PDP na dauke da wata cuta da ba ta da magani, babu wata ƙwayar magani da za ta iya warkar da abinda ke damunta.
"Ba ma son mu shiga wani gida da ba za a iya gyara shi ba. Saboda haka PDP ba ta cikin jerin zabinmu."
- Babachir Lawal.
Wannan furuci na Babachir na zuwa ne a daidai lokacin da manyan jagororin adawa ke ci gaba da taruka da nufin haɗewa wuri ɗaya domin kawo ƙarshen mulkin APC a 2027.
Atiku zai sake tsayawa takara a 2027?
Game da yiwuwar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi takara, Babachir Lawal ya ƙara da cewa:
“Kamar kowa, yana da ’yancin yin takara. Ba aikin na ba ne in yanke hukuncin kan jam’iyyar da zai tsaya takara a inuwarta, wannan shi da mashawartansa ne za su yanke.”

Asali: Twitter
Sai dai tsohon sakataren gwamnatin tarayya, wanda ya yi aiki a zamanin Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa da Atiku ake shirye-shirye kafa haɗaka.
"Tabbas na hadu da Alhaji Atiku Abubakar a yawancin tarurrukan da muka yi dangane batun hadewar jam’iyyu ko kafa sabuwar jam’iyya.
"Don haka yana cikin wadanda ke da kishin ganin an samu jam’iyyar adawa guda daya mai karfi," in ji shi.
Sanatocin PDP sun faɗi sharaɗin shiga haɗaka
A wani rahoton, mun kawo cewa sanatocin PDP sun bayyana cewa a shirye suke su shiga haɗaka don kifar da Bola Tinubu a 2027 amma bisa sharaɗi.
Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro ne ya sanar da hakan bayan taron da suka yi a Abuja ranar Talata.
Ya ce duk wani ƙawance da za a ƙulla a siyasa, kamata ya yi a ce jam'iyyu ne suke jagoranta ba wasu tsirarun mutane ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng