Ta Faru Ta Kare: Gwamnati Za Ta Yi Gwanjon Gidaje 753 da Aka Kwato daga Emefiele

Ta Faru Ta Kare: Gwamnati Za Ta Yi Gwanjon Gidaje 753 da Aka Kwato daga Emefiele

  • A ranar Talata, gwamnatin tarayya ta ce za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta kwato daga Godwin Emefiele a Cadastral Zone, Abuja
  • Kotu ta tabbatar da ƙwace gidajen a 2024, yayin da shugaban EFCC Olanipekun Olukoyede ya ce hakan nasara ce a yaki da rashawa
  • Ministan gidaje, Ahmed Dangiwa ya ce za a yi gwanjon gidajen ta shafin Renewed Hope, bayan kammala abubuwan da suka rage

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ta na sayar da gidaje 753 da aka kwato daga hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Hukumar EFCC ce ta mika gidajen, da ke cikin yankin Cadastral na birnin tarayya Abuja, ga ma’aikatar gidaje da ci gaban birane, a ranar Talata.

Gwamnatin tarayya ta karfi gidaje 753 da EFCC ta kwato daga hannun tsohon gwamnan CBN
Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede yayin mika gidaje 753 da aka kwato daga Emefiele ga gwamnati. Hoto: @Arch_Dangiwa
Asali: Twitter

EFCC ta mika gidajen Emefiele ga gwamnati

EFCC ta kwace gidajen, da suka haɗa da manya da kanana, a matsayin wani ɓangare na binciken da ake gudanarwa kan Emefiele, inji rahoton Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun babban birnin tarayya da ke Apo a Abuja ta yi watsi da ƙarar Emefiele da ke neman mallakar gidajen, bayan da ta bayar da umarnin wucin-gadi da kuma na ƙarshe na ƙwace kadarorin a Disamba 2024.

Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya ce mika kadarorin ga gwamnati yana nuna sahihancin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

“Wannan mika kadarorin hujja ce ta ainihin nasarorin da ake samu a yaki da cin hanci da laifuffukan kuɗi,” inji Olukoyede.

Tinubu ya ba da umarnin kammala gina gidajen

Ministan gidaje da ci gaban birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya ce za a sayar da kadarorin ga jama’a ta hanyar yin gwajo bisa tsari na gaskiya.

A shafinsa na X, Dangiwa ya bayyana cewa:

“Ina farin cikin karɓar bakuncin shugaban EFCC, Mista Olukoyede, yayin da ya mika gidaje 753 da aka kwato daga tsohon gwamnan CBN ga ma’aikatar gidaje.

Ya bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da umarnin Shugaba Bola Tinubu na cewa a kammala gine-ginen sannan a sayar da su.

Dangiwa ya ce ma’aikatar za ta gudanar da binciken ƙarfin gine-ginen da kayan aikin da ke ciki, domin tabbatar da inganci da aminci ga masu siya.

EFCC ta mika takardun gidae 753 da ta kwato daga tsohon gwamnan CBN, Godwin Emiefele
Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede yayin mika gidaje 753 da aka kwato daga Emefiele ga gwamnati. Hoto: @Arch_Dangiwa
Asali: Twitter

Yadda gwamnati za ta sayar da gidajen

Ya ƙara da cewa za a kammala ayyukan gine-ginen da suka rage, irin su hanyoyi da magudanan ruwa, domin sauƙaƙa rayuwa a unguwar.

Ya bayyana cewa:

Ministan ya tabbatar cewa za a sayar da gidajen ta hanyar amfani da shafin yanar gizo na Renewed Hope, inda ake gwanjon kadarorin gwamnati.

“Za mu hada gwiwa da EFCC domin nuna cewa yaki da rashawa na iya haifar da ci gaba mai amfani, ta hanyar juya kadarorin da aka sace zuwa gidajen zama ga 'yan Najeriya.”

- Ahmed Musa Dangiwa.

Kotu ta kwace wa Emefiele kadarorin N11bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin kwace wasu manyan kadarori da kuɗaɗe da ake zargin mallakin Godwin Emefiele ne.

Mai shari’a Chukwujekwu Aneke ne ya bayar da umarnin ranar Laraba, 5 ga Yuni, 2024 bisa buƙatar da hukumar EFCC ta gabatar gaban kotun.

EFCC ta bayyana cewa tsohon gwamnan CBN ɗin ya mallaki kadarorin ne ta hanyar da ba ta dace ba, bisa zargin almundahana da satar kuɗin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.