Kotu Ta Yi Hukunci kan Rusau, An Ci Tarar Gwamnatin Jihar Kano N2.6bn
- Kotu a Kano ta soke kwace da rusa kamfanin Tiamin da gwamnatin jihar ta yi wanda aka yi lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje
- Kotun ta kuma umarci gwamnati ta biya diyyar Naira biliyan 2.6 saboda asarar da aka jawo wa kamfanin bayan rushe-rushen da aka yi
- Mai shari’a Ibrahim Karaye ne ya yanke hukuncin, ya jero ka'idojin da gwamnatin Kano ta take yayin gudanar da rushe-rushen
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wata babbar kotun Kano ta soke kwace filin da gwamnatin jihar ta yi wa kamfanin Tiamin Multi Services Global Limited.
Kotun ta kuma umarci gwamnatin Kano da ta biya kamfanin diyya kudi har Naira biliyan 2.6.

Asali: UGC
Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa filin da ake gardama a kai yana kan titin Court Road, unguwar Gyadi-Gyadi a karamar hukumar Tarauni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuma gwamnati ta soke shi tare da rusa gine-ginen da ake yi a kai tun a lokacin mulkin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Alkali ya yi hukunci kan rusau a Kano
Rahoton ya ce bayan rusa gine-ginen, kamfanin ya garzaya kotu yana neman diyya kan kawo masa tasgaro a aikinsa, tare da mayar da aikinsa baya.
A hukuncin da Mai shari’a Ibrahim Karaye ya yanke a ranar Laraba, ya bayyana cewa soke filin da ikon mallaka ya sabawa doka kuma wamnatin ba ta da hurumin yin hakan.

Asali: Facebook
Alkalin ya ce takardar sanar da soke filin da ofishin kula da filaye na jihar Kano ya aike a ranar 3 ga Satumba, 2021, ba ta bi ka'ida ba.
Ya ce sanarwar ba ta zo da wata sanarwa ko damar kare kai ga mai filin ba, lamarin da ya saba wa dokar amfani da filaye.
Alkali ya ci tarar gwamnatin Kano
Mai shari’a Ibrahim Karaye ya kuma soki gwamnati da ta shiga ta karfi da yaji ta rusa gine-ginen da suka ci miliyoyin Naira duk da cewa karar tana gaban kotu a lokacin.
Mai shari’a Karaye ya bayyana cewa:
“Takardun mallakar filin wato LKN/COM/2017/116 (wanda aka sake tabbatar da shi a matsayin LPKN 1188), MLKN01622 da MLKN01837 suna nan da inganci kuma ba su lalace ba.”
Kotun ta bayyana cewa:
"Soke ikon mallakar kamfanin a filin da ke kan titin Court Road, Gyadi Gyadi, a karamar hukumar Tarauni, bisa takardun mallaka LKN/COM/2017/116 (LPKN 1188), MLKN01622 da MLKN01837 da aka bayyana a taswirar TP-KN-105E da TP-KNUPDA-105E, ta hanyar wata wasika daga babban sakatare a hukumar kula da filaye ta jihar Kano (wanda ke matsayin wanda ake kara na uku), a ranar 3 ga Satumba, 2021, ba tare da sanarwa ba, ya saba kundin tsarin mulki, ba shi da inganci kuma babu wani tasiri na doka da ya ke da shi.”
Kotun ta bayar da hukunci cewa a biya kamfanin Tiamin Naira biliyan 2.125 a matsayin diyya ta musamman kan kudin da kamfanin ya kashe wajen gina gine-ginen.
Sai kuma karin Naira miliyan 500 a matsayin diyya gaba daya kan rusau da aka yi ba bisa ka’ida ba, da Naira miliyan 10 a matsayin kudin shigar da kara.
Rusau ya zo da tangarda a jihar Kano
A baya, mun wallafa cewa mutane huɗu sun rasa rayukansu a garin Rimin Auzinawa da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano, sakamakon wani rikici.
An samu matsala ne yayin da ma’aikatan KNUPDA ke rusa gine-gine, inda jami’an tsaron suka bude wuta, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.
Rahotanni sun ce mazauna yankin sun fusata ne bayan rushewar gidajensu, lamarin da ya jawo tashin hankalin har jami'an suka bude wuta a kan bayin Allah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng