Karuwar Ta'addanci: Gwamnoni Sun Yi Ganawar Sirri da Babban Hafsan Tsaro
- Gwamnonin Najeriya sun gudanar da taro da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, domin tattauna matsalolin tsaro a ƙasa
- Taron ya gudana a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq
- An tattauna kan yadda za a magance hare-hare, sace-sace da kisan kai da ke yawaita a sassa daban-daban na ƙasar, musamman Filato
- Gwamnonin jihohin Borno, Ekiti, Adamawa, Kaduna, Bayelsa, Gombe, Ogun, Imo, Oyo, Ondo, Benue, Nasarawa da Filato sun halarci taron
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnonin Najeriya sun gudanar da wani zama na musamman da Babban Hafsan Tsaro na ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa.
Taron ya mayar da hankali ne kan tattaunawa game da ƙalubalen rashin tsaro da ake fuskanta a ƙasar.

Asali: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa shugaban taron shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An maida hankali kan lamurra da suka shafi sace mutane, hare-hare da kisan gilla da suka ƙaru kwanan nan.
Gwamnoni sun gana da babban hafsan tsaro
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa tattaunawar ta fi karkata ne kan matsalolin tsaro da ke addabar wasu jihohi kamar su Filato, Benue da sauran su.
Duk ba a a fitar da cikakken bayanin tarin ba, an tattauna ne domin samo mafita kan yadda za a dakile karuwar tashin hankali.
Gwamnonin Jihohin da suka zauna da hafsan tsaro
Gwamnoni daga jihohin Borno, Ekiti, Adamawa, Kaduna, Bayelsa, Bauchi, Gombe, Ogun da Imo sun halarci taron. Sauran jihohin da suka halarci taron sun haɗa da Oyo, Ondo, Benue, Nasarawa da Filato, tare da mataimakan gwamnonin jihohin Neja da Enugu.

Asali: Facebook
Ministan gidaje da ci gaban Birane, Ahmed Dangiwa, shi ma yana daga cikin mahalarta taron.
Wannan zama na zuwa a lokacin da hare-haren yan bindiga suka karu a jihar Filato, Binuwai da Borno.
Gwamnonin sun koka da cewa masu aikata ta'addancin sun mamaye wasu yankuna a jihohinsu.
Tinubu ya zauna da shugabannin tsaro
Ganawar gwamnonin da Janar Christopher Musa na zuwa ne awanni kadan bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da jagororin tsaro
Bola Ahmed Tinubu ya nuna rashin jin daɗinsa matuƙa kan yadda kashe-kashe da hare-hare ke ci gaba da faruwa a jihohin Borno, Binuwai da Filato.
A ganawar da aka yi ta kusan sa’o’i biyu, Tinubu ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a dakatar da wannan al’amari da ya jima yana addabar al’umma.
An shawarci gwamnati kan rashin tsaro
Dr. Ibrahim Tanko Wudilawa, tsohon kwamandan rundunar haɗaka ne a Kano, ya shaidawa Legit cewa kishin kasa ne sinadarin farko na kakkabe ta'addanci.
Ya ce:
"Wannan rashin tsaron da ake samu, duka shiryayyun hare-hare ne. Harkar tsaron nan, idan ana so a inganta ta dole sai an sa kishin kasa, kuma an cire duk wadanda ba su da kishin kasa. Komai matsayinka a gwamnati, ko ba ka da kishin kasa na inganta tsaro a kasar ka, ba ka da amfani."
"Dazukan kasar nan, kowa ya san su, kuma hare-haren da ake kawo wa, duka ta dazukan ne, saboda haka dole ne a inganta tsaro a dazukan."
Ya kara da cewa gwamnati ta fi kowa sanin yadda za a aika dakarun da za su tabbatar da kakkabe miyagun dake neman mafaka a dazukan.
Dr. Wudilawa ya kuma ce akwai bukatar a yi amfani da kungiyoyi da kai wajen fatattakar ta'addanci, matukar ana son dawo da zaman lafiya.
Babban hafsan tsaro ya magantu kan ta'addancin
A baya, kun ji cewa Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ta kuduri aniyar kawo karshen matsalar tsaro.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a wani taron addu’a na musamman da aka gudanar a Kudancin Kaduna, wanda kungiyar Southern Kaduna Solemn Assembly ta shirya.
A cewarsa, rundunar sojin Najeriya za ta yi amfani da dukkan kayan aiki da ke hannunta domin kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu a fadin ƙasar.
Asali: Legit.ng