Magana Ta Tabbata, Gwamnatin Tinubu Ta Biya Bashin Dala Miliyan 3.4 da Buhari Ya Karɓo

Magana Ta Tabbata, Gwamnatin Tinubu Ta Biya Bashin Dala Miliyan 3.4 da Buhari Ya Karɓo

  • Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da kammala biyan bashin asusun ba da lamuni (IMF)
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na ƙasa, Mohammed Idris ne ya sanar da hakan da yake hira da manema labarai bayan taron FEC
  • A kwanakin baya ne IMF ya cire sunan Najeriya a jerin kasashe masu tasowa da yake bi bashin kudi, lamarin da masana suka ce babban ci gaba ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da biyan bashin Dala biliyan 3.4 da ta karɓa daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF) a lokacin annobar cutar Korona watau COVID-19.

Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama'a na Ƙasa, Mohammed Idris, ne ya tabbatar da haka a yau Litinin, 12 ga watan Mayu, 2027.

Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris.
Gwamnatin Tarayya ta biya bashin da ta karɓo daga IMF Hoto: @FedMinoimf
Asali: Twitter

Channels tv ta rahoto cewa ministan ya faɗi hakan ne yayin da yake wa manema labarai bayani bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da aka gudanar a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta biya bashin da Buhari ya karɓo

"Mun gama biyan dukkan bashin Dala biliyan 3.4 da aka karɓa daga IMF lokacin COVID-19, kuma wannan ya nuna yadda gwamnati ke ta ƙoƙarin tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasa ya daidaita," in ji Ministan.

Rahoton IMF da aka fitar kwanan nan ya nuna cewa Najeriya ta fita daga jerin kasashen da asusun ba da lamunin ke bi bashi.

A cewar masana, wannan lamari babban nasara ne a bangaren kula da kasafin kudi da bashi na Najeriya.

IMF ya cire Najeriya daga jerin kasashe 91

Daga cikin kasashe 91 masu tasowa da suka runtumo bashi daga hannun IMF, Najeriya ba ta cikin jerin a watan Mayu 2025, alamar cewa ta kammala biyan dukkan basussukan da ta karɓa.

Tun daga 2023, Najeriya ta fara rage bashin wanda a lokacin ya dawo Dala biliyan 1.61. A watan Janairu 2025, ya sauka zuwa dala miliyan 472.

A ƙarshe kuma Najeriya ta samu damar kammala biyan bashin gaba ɗaya a watan Mayun da muke ciki.

Shugaba Tinubu.
Yadda Najeriya ta biya bashin IMF Hoto: @aonanuga1956
Asali: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta tabbatar da lamarin

Bayan cire sunan Najeriya a jerin kasashen da asusun IMF ke bi ba shi, a yanzu gwamnatin tarayya ta tabbatar da kammala biyan kuɗin a hukumance.

Bayan taron FEC yau Litinin, ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya ce Najeriya ta fita daga ƙasashen da IMF ke bi bashi, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Tinubu ya faɗi yadda ya karɓi kasa a 2023

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda ya gaji baitul-malin Najrriya daga hannun Muhammadu Buhari.

Shugaba Tinubu ya ce lokacin da ya karɓi mulki a watan Mayu, 2023, ya tarar da lalitar gwamnati kusan babu ko kwandala da kuma tarin matsaloli.

Ya ce lokacin da ya hau mulki, kasar na fama da dimbin basussuka, tallafin da ba za a iya jurewa ba, da tsarin musayar kudi mara kan-gado.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262