Lokaci Ya Yi: Ana Zargin Wata Budurwa Ta Yi Ajalin Mutane 3 da Taliya a Jihar Katsina
- Mutum huɗu ƴan gida ɗaya sun ci taliyar da ake zargin an sa guba a ciki, uku daga ciki sun riga mu gidan gaskiya a jihar Katsina
- An tattaro cewa ƴan sanda sun kama wacce ta dafa abincin tare da wasu mutum biyu da hukuma ta fara bincikensu kan lamarin
- Rundunar ƴan sandan reshen Katsina ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba, amma an ce mace ɗaya na kwance a asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Mutane uku, ciki har da ƙananan yara, sun rasu sakamakon cin abincin da ake zargin an zuba guba a yankin Magama Jibia da ke Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne bayan wata budurwa mai suna Fatima Abdulƙadir ta dafa taliya ta ba yaran ƴan gida ɗaya suka ci, mutum uku sun mutu, ɗaya na kwance a asibiti.

Asali: Getty Images
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum 3 ƴan gida ɗaya sun rasu a Katsina
Bisa ga bayanan da ya fitar, wadanda suka rasu sun hada da Hussaina Ayuba, Ahmed Ayuba, da Nana Ayuba.
Tun farko ya ce an yi ƙoƙarin taimaka masu da aka garzaya da su zuwa Asibitin Gwamnati na Jibia bayan sun ci taliyar spaghetti da ake zargin an sa wa guba.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa uku daga ciki sun mutu a asibitin yayin da mace ɗaya mai suna Hafsan Ayuba, ke kwance har yanzu ana mata magani.
Binciken ya nuna cewa wata budurwa mai shekaru 20 da haihuwa, Fatima Abdulkadir, ita ce ya dafa taliyar da suka ciki.
An kama budurwar da ta dafa abincin
Majiyar ta ce yanzu haka ƴan sanda sun kama Fatima tare da wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a zuba gubaa a abincin.
Ya bayyana cewa:
“Wadanda suka mutu sune Hussaina Ayuba, Ahmed Ayuba, da Nana Ayuba, bayan da suka ci abinci da ake zargin an sa wa guba. Hafsat Ayuba na ci gaba da jinya.”

Asali: Twitter
‘Yan sanda sun kai ziyara wurin da abin ya faru, yayin da aka mika gawarwakin wadanda suka mutu ga ‘yan uwansu domin yi masu jana'iza bisa tsarin Musulunci.
Babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ‘yan sandan jihar Katsina har kawo yanzu da muka haɗa wannan rahoto.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sanda, Abubakar Aliyu, ta wayar salula ya bukaci a tura masa saƙo amma har yanzu bai turo da amsa ba.
Mutum 4 sun ci guba a jihar Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa mutane huɗu ƴan gida ɗaya mutu bayan sun ci guba a abinci a jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya.
Lamarin na baya-bayan ya faru ne a safiyar ranar Alhamis a kauyen Olori a Banni, karamar hukumar Kwara ta Arewa.
Hukumar NSDC ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma ta umarci duk wanda ya ci abincin a gidan su gaggauta kai kansu asibiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng