'Yan Bindiga Sun Addabi Mutane da Hare Hare a Kogi, an Sake Yin Barna

'Yan Bindiga Sun Addabi Mutane da Hare Hare a Kogi, an Sake Yin Barna

  • Wasu ƴan bindiga sun sake kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi
  • Ƴan bindigan waɗanda suka ɗauke da makamai sun yi awon gaba da mutum huɗu bayan sun kai farmaki cikin ƙauyen Ofoloke
  • Sabon harin na ƴan bindigan ya fara tilastawa mutanen ƙauyen daga gidajensu saboda addabar su da ake yi da hare-hare

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a jihar Kogi.

Ƴan bindigan sun sace mutane huɗu a ranar Talata a garin Okoloke, da ke ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi.

'Yan bindiga sun kai hari a Kogi
'Yan bindiga sun sace mutane a Kogi Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce wannan harin na baya-bayan nan ya kai adadin mutanen da aka sace a cikin wannan ƙauyen zuwa mutum takwas cikin kwanaki bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun takura da hare-hare a Kogi

Tun da fari, ƴan bindiga sun sace basaraken ƙauyen Ofoloke, wanda ya ke da shekaru 91, mai martaba Oba Dada James Ogunyanda, a fadarsa a ranar Alhamis da ta gabata misalin karfe 2:00 na dare.

Masu garkuwa da mutanen sun fara neman kuɗin fansa Naira miliyan 100, wanda daga baya suka rage zuwa Naira miliyan 50.

Bayan kwana uku da faruwar hakan, a ranar Asabar, wasu ƴan sa-kai mutum uku, sun rasa rayukansu a wani artabu da masu garkuwa da mutane a cikin ƙauyen.

Ƴan bindiga sun sake sace mutane

Harin na baya-bayan nan ya faru ne a safiyar ranar Talata lokacin da ƴan bindigan suka mamaye yankin, inda suka kuma sace mutane huɗu, ciki har da wani shahararren jagoran al’umma.

'Yan bindiga sun yi barna a Kogi
'Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Kogi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wani mazaunin ƙauyen mai suna James Ogundele, ya tabbatar da ɓarnar da ƴan bindigan suka yi, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

"Ƴan bindiga sun sake shigowa garinmu, kai tsaye suka nufi gidan Ezekiel Durojaiye, wani tsohon ma’aikaci wanda ya yi ritaya kuma jagoran al’umma da ke ƙauyen Okunran, kusa da Ofoloke.

“A ranar Alhamis da ta gabata, ƴan bindiga sun sace basaraken ƙauyen, Oba James Dada Ogunyanda. A ranar Asabar kuma, an sace wasu ƴan sa- kai biyu da wani ma’aikacin kamfanin sadarwa."
"Tare da wannan harin na baya-bayan nan, yanzu mutane takwas ne aka sace daga wannan ƙauyen cikin mako guda."

- James Ogundele

Rahotanni sun nuna cewa a safiyar ranar Laraba, mutane da dama sun fara barin garin sakamakon tsananin hare-haren da ake kai musu.

Iyalan basarake sun fara neman taimako

A wani labarin kuma, kun ji cewa iyalan basaraken da ƴan bindiga sun fara neman taimako domin haɗa kuɗin fansar da za su ceto shi.

Iyalan Dada James Ogunyanda sun buƙaci jama'a da ƙungiyoyi da su kawo musu agaji domin haɗa kuɗaɗen fansan da ƴan bindiga suke buƙata.

Hakazalika sun nuna takaicinsu kan yadda gwamnati da ƴan siyasar yankin Kogi ta Yamma suka ƙi kawo musu ɗauki domin a samu a ceto dattijon.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng