Bayan 11 sun mutum da farko, mutum 4 ƴan gida ɗaya sun sake mutuwa bayan cin abinci mai guba a Kwara

Bayan 11 sun mutum da farko, mutum 4 ƴan gida ɗaya sun sake mutuwa bayan cin abinci mai guba a Kwara

  • Mutane hudu yan gida daya sun riga mu gaskiya bayan cin abinci mai guba a jihar Kwara
  • Hukumar tsaro da NSCDC reshen jihar Kwara ta tabbatar da hakan ta bakin kakakinta
  • Rahotanni sun ce mutum hudun da suka rasu yan gida daya ne da wasu 11 da suka mutu a baya

Wasu mutane hudu yan gida daya sun mutu sakamakon guda da suka ci a abinci, wata daya bayan wasu mutum 11 yan gidan sun mutu bayan shan maganin gargajiya, hukumar tsaro ta NSCDC ta tabbatar.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin na baya-bayan ya faru ne a safiyar ranar Alhamis a kauyen Olori a Banni, karamar hukumar Kwara ta Arewa a jihar Kwara.

Taswirar Jihar Kwara
Taswirar Jihar Kwara. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

Kakakin NSCDC na jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya ce:

"Mun samu labarin rasuwar yaran Alhaji Mohammed Abubakar biyu a kauyen Olori, Banni a karamar hukumar Kwara ta Arewa; Umar Mohammed dan shekara 25 da Kadir Mohammed dan shekara 18.

"Sun fara amai ne misalin karfe 4 na safen ranar Alhamis aka garzaya da su babban asibitin Igbeti a jihar Oyo.

"An gwada su aka gano sun ci abinci mai guba ne.

"Bayan mintuna kadan, su biyun suka mutu a yayin da ake shirin birne su, daya daga cikin jikokin Abubakar, Umar Mohammed shima ya mutu."

KU KARANTA: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Kakakin ya ce babban jami'in hukumar na yankin, Taofeek ya shawarci sauran yan gidan da suka ci abinci iri daya da wadanda suka rasu su tafi asibiti a yi musu gwaji.

Wasu mazauna garin da suka yi magana da Daily Trust sun yi kira ga hukumomi su saka ido a kan lamarin duba da cewa sau biyu irin wannan mace-macen ya faru cikin wata daya a kananan hukumomi biyu a Kwara ta Arewa.

Saliu Zakari, wani mazaunin garin ya ce:

"Wannan abin damuwa ne akwai bukatar hukuma ta yi bincike a kan lamarin. Mun rasa mutane 11 a Baruteen saboda maganin gargagiya, rannan kuma mutum hudu yan gida daya dukkansu yan uwa sun sake mutuwa."

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel