Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

  • Rundunar yan sanda ta kama wani mutum da ke karyar cewa shi mataimakin kwamishinan yan sandan ne a Kano
  • An kama mutumin ne mai shekaru 45, Mohammed Aliyu mazaunin Mariri Hotoro Quarters bayan ya tafi otel yana neman a yi masa rangwame
  • Manajan otel din bai gamsu da halayansa ba hakan yasa ya tuntubi rundunar yan sandan Kano daga nan aka kama shi

Rundunar ƴan sanda na jihar Kano ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda na bogi a wani otel a birnin Kano, The Punch ta ruwaito.

LIB ta ruwaito cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Alhamis.

Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama a cikin otel a Kano
ACP na yan sanda na bogi da aka kama a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO ba

Haruna ya ce an kama wanda ake zargin, wani Mohammed Aliyu mazaunin Mariri Hotoro Quarters bayan ya gabatar da kansa a matsayin ACP a wani otel a Kano ya kuma nemi a bashi ɗaki ya sauki baƙinsa da ke zuwa daga Kaduna.

Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama a cikin otel a Kano
ACP na yan sanda na bogi da aka kama dauke da takardun bogi a otel a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama a cikin otel a Kano
Mutumin da aka kama yana karyar cewa shi ACP ne na yan sanda a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

A cewar Haruna:

"A ranar 20/07/2021 misalin ƙarfe 6 na yamma, ingantaccen bayani ya nuna cewa wani Mohammed Aliyu ɗan shekaru 45 mazaunin Hotoro Mariri Quarters ya gabatar da kansa a matsayin kwamishinan ƴan sanda a wani otel a Kano.
"Ya nemi a bashi ɗaki da zai sauki baƙinsa da ke zuwa daga Kaduna da wasu sassan kasar, kuma yana son a yi masa rangwame a matsayinsa na babban ɗan sanda mai muƙamin ACP.
"Ya bawa manajan otel ɗin katinsa mai ɗauke da sunansa a matsayin mataimakin kwamishinan ƴan sanda kuma kwamandan 52 PMF Challawa, Kano.
"Ya kara da cewa DPO na Nassarawa ƙaninsa ne a Rundunar Yan sandan kuma ya taba yin aiki a karkashinsa.
"Bayan lura da wasu halaye da bai gamsu da su ba, manajan otel ɗin ya sanar da rundunar yan sanda nan take hakan yasa aka kama wanda ake zargin."

KU KARANTA: Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara

Kakakin yan sandan ya kuma ce an samu wasu takardun jabu a tare da shi mai ɗauke da sunan Ibrahim Muhammad Tijjani a matsayin likita.

Haruna ya ce an tura wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifukan na SCIID.

An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

A wani labarin, Ƴan sanda a jihar Niger sun yi holen wasu mutane uku da ake zargi da mallakar kudaden jabu ƴan dubu-dubu da adadinsu ya kai Naira miliyan 15.8, Guardian NG ta ruwaito.

Wadanda ake zargin sune Fasto Sabastine Dabu, ɗan shekara 48 daga Zuru, jihar Kebbi, Emmanuel Aka Zuwa, ɗan shekara 42 daga ƙauyen Adi, ƙaramar hukumar Buruku, jihar Benue da Umar Mohammed, ɗan shekara 50 daga Pandagori, ƙaramar hukumar Rafi, jihar Niger.

Guardian ta ruwaito cewa yayin holen wadanda ake zargin a hedkwatar yan sanda a Minna, kakakin yan sanda Wasiu Abiodun ya yi bayanin cewa ƴan sandan ƙaramar hukumar Kontagora, jihar Niger ne suka kama su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: