Mutuwa Ta Kawo Tsaiko a Shari'ar Abba Kyari kan Zargin Safarar Ƙwayoyi a Abuja
- An dage shari’ar DCP Abba Kyari bayan rasuwar ‘yar lauya Onyechi Ikpeazu, wacce za a karrama bayan ta mutu a hatsarin mota
- Lauyan gwamnati ya ce babu tiyatar da aka yi wa Kyari, amma lauya mai kare shi ya bukaci kotu ta yi watsi da wannan zargin
- Alkalin kotu ya dage sauraren karar har 7 ga Yuli domin bai wa lauya Dr. Ikpeazu lokaci ya murmure daga bakin cikin da ya ke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An samu tsaiko a shari'ar da ake yi a Abuja kan dakataccen dan sanda, DCP Abba Kyari.
Mutuwar wata yar babban lauya da ke kula da shari'ar ta tilasta dage zaman kotun da aka yi niyyar yi a yau Laraba.

Asali: Facebook
An dage shari'ar Abba Kyari da ake yi
Tribune ta ce rasuwar ‘yar Dr. Onyechi Ikpeazu, SAN bayan hatsarin mota ta hana ci gaba da shari’ar Kyari da wasu a kotun tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tsara Kyari da abokan tuhumarsa su fara kare kansu a ranar Laraba, amma lauyan da ke wakiltar Ikpeazu ya ce ya yi rashin ‘yarsa.
Abdul Mohammed, SAN, ya shaida wa Mai Shari’a Emeka Nwite cewa ‘yar Ikpeazu da za a karrama a matsayin lauya, ta mutu a hadarin mota ranar Asabar.
Ya ce:
“Saboda girmamawa ga kotu, ya aiko ni in sanar da ku wannan bakin labari tare da bukatar jinkiri domin ya samu sauki.
“Mun keɓance ranar 7 ga Yuli domin muna ganin lokacin zai isa ya murmure kafin ya cigaba da kare wadanda ake tuhuma."
Lauyan gwamnati, Sunday Joseph ya ce ya yi bakin ciki da jin rasuwar ‘yar lauyan kuma ya amince da ranar da aka ba da shawara.
Mohammed ya ce wannan zargi kamar cin mutuncin ɗan uwansu lauya ne, ya bukaci kotu ta yi watsi da shi saboda babu hujjar doka a kai.
Ya ce:
“Idan yana da hujja, sai ya zo da takarda na doka, amma yanzu haka zarginsa bai dace ba."

Asali: Twitter
Yaushe za a dawo kotu kan shari'ar Kyari?
Kyari ya nuna wa kotu inda aka yi masa tiyata a ciki kuma kotu da masu shari’ar sun ga inda aka daure cikinsa da bandeji.
Alkalin ya ce:
“Duk da halin da muke ciki, babu wani abu da za mu iya yi yanzu. Idan akwai matsala, a kawo bukata cikin doka.”
Daga nan ne kotu ta dage sauraren karar zuwa 7 ga Yuli, 2025, domin ci gaba da kare kai daga wadanda ake zargi.
A baya, kotu ta ce an gamsu cewa NDLEA ta gabatar da hujjoji da suka isa su sa wadanda ake zargi su kare kansu.
Abba Kyari, wanda shi ne shugaban IRT a baya, an kama shi ranar 14 ga Fabrairu, 2022, bayan NDLEA ta bayyana shi da hannu a safarar kwaya.
Iyalan Abba Kyari sun kare shi
Kun ji cewa wasu daga cikin iyalan Abba Kyari sun karyata zargin yana da asusun banki guda 10 dauke da N200m.
Iyalan suka ce labarin karya ne da aka shirya amma sun ce yana da asusu a bankuna hudu kawai da jimillar kudin da bai kai N4m ba.
Shaida a kotu ya tabbatar babu wata alaka tsakanin kudin asusun Kyari da wata haramtacciyar hulɗa ko laifi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng