Abba Kyari: An cigaba da shari’a, NDLEA ta gabatar da hujjojin kwayoyi da Daloli

Abba Kyari: An cigaba da shari’a, NDLEA ta gabatar da hujjojin kwayoyi da Daloli

  • Hukumar NDLEA ta kira mutum uku da ya bada shaida a kotu a shari’ar ta da su Abba Kyari
  • Wani jami’in NDLEA ya nunawa kotu $61,400 da aka nemi a biya a matsayin kudin cin hanci
  • Peter Joshua ya zo da hodar iblis da ake zargin an karbe daga hannun wadanda ake kara

Abuja - A jiya ne Hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta bayyana da karin wasu hujjoji gaban kotun tarayya da ke garin Abuja.

This Day ta ce hujjojin da aka gabatar a ranar Laraba 20 ga watan Yuli 2022, sun hada da makudan kudin kasar waje har $61, 400 da kwalaye 24 na hodar iblis.

Kamar yadda aka fadawa Alkali, an yi amfani da wannan $61,400 wajen bada cin hanci ga jami’an NDLEA da suka kama wadanda ake zargi da safarar kwayoyin.

Kara karanta wannan

Jerin bambanci 10 da ke tsakanin saida kamfanin NNPC da yin kasuwanci da NNPC

Su kuma tulin hodar iblis da aka kai kotu, su ne wanda ake shari’a da su Abba Kyari a kan su.

Cin hancin kusan N250m

Lauyoyin hukumar NDLEA sun yi ikirarin DCP Kyari ya yi yunkurin ba wani babban jami’i cin hancin fam Dala 61, 400. 00 a wani wurin cin abinci a garin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fadawa kotu cewa ‘dan sandan ya tunkari jami’in na NDLEA da wannan kudi da sun kai N250m ne da nufin birne maganar wasu da ake zargi da harkar kwaya.

Abba Kyari Hoto: www.nigerianeye.com
DCP Abba Kyari a kotu Hoto: www.nigerianeye.com
Asali: UGC

Peter Joshua ya bada shaida

A kokarin gamsar da kotu, NDLEA ta kira mai bada shaidanta na uku a karar, Peter Joshua wanda babban jami’i ne na hukumar mai aiki a birnin tarayya Abuja.

Peter Joshua ya shaidawa kotu cewa an damka masa wannan kudi a ranar 25 ga watan Junairu, bayan ya yi gwaji a kan wasu kaya da ake zargin kwayoyi ne.

Kara karanta wannan

Gwajin da aka yi wa sinadarin da aka gano a hannun Kyari Hodar Iblis ne - NDLEA

Mai bada shaidar ya ce an karbe kwayoyin ne daga hannun Chibunna Umeibe da Emeka Ezenwane, wadanda ake tuhuma da laifi yanzu haka tare da Abba Kyari.

Jami’in ya ce kudin duka ‘yan $100 ne a cikin wata leda mai shara-shara. An kirga Dalolin a gaban kowa a kotu kamar yadda Alkali Daniel Emeka Nwite ya bukata.

Vanguard ta ce baya ga Daloli, Joshua ya kawo kulli 24 na hodar iblis a jakunkuna. Alkali ya karbi wadannan hujjoji ganin Lauyoyin da ke bada kariya ba su da ja.

Abba Kyari suna tsare

Hukumar ta NDLEA ta na zargin DCP Abba Kyari da laifin harka da miyagun kwayoyi, don haka ake shari’a da jami’in ‘dan sandan da yanzu yake a garkame.

A watan Maris, an samu rahoto kotu ta ki bada belin 'dan sandan. Alkali ya duba maganar NDLEA, ya ga bai dace a bada belinsa kamar yadda Lauya ya nema ba.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun bada shawarar a gurfanar Shugaban APC a kotu bayan bincike

Asali: Legit.ng

Online view pixel