Sarki Sanusi II da Abokan Karatunsa Sun Ziyarci Cibiyar Sararin Samaniyar Amurka
- Mai Martaba Sarki, Khalifa Muhammad Sanusi II ya kai ziyara birnin Houston da ke Texas a kasar Amurka inda ya hadu da tsofaffin abokansa
- Muhammadu Sanusi II ya ziyarci cibiyar sararin samaniya ta NASA tare da sauran ‘yan kungiyar tsofaffin daliban makarantar da suka yi a Lagos
- Sanusi II ya halarci liyafar da aka shirya musu da dare a Houston tare da fitattun mutane ciki har da Sanata Bukola Saraki da Dr Oluyinka Olutoye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Mai Martaba Sarki, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya kai ziyara ta musamman zuwa birnin Houston da ke jihar Texas a Amurka.
Sarkin ya shaida wani gagarumin taro da aka gudanar tare da tsofaffin ɗaliban makarantar King's College Lagos.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da masarautar Kano ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ziyarar ta zo ne bayan ya jagoranci bikin tashi jirgin farko na alhazan jihar Kano zuwa ƙasar Saudiyya a ranar Laraba, 14 ga Mayu, 2025, a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
A Houston, Sanusi II ya kasance bako na musamman a tarukan da suka haɗa da ziyartar cibiyar binciken sararin samaniya ta NASA da kuma liyafar dare da aka shirya.
Sanusi II ya ziyarci cibiyar NASA a Amurka
A ranar Juma’a 16 ga Mayu, 2025, Mai Martaba Sanusi II ya kai ziyara cibiyar sararin samaniya ta NASA da ke Houston.
Sarkin ya kai ziyarar ne tare da tsofaffin ɗaliban makarantar King's College Lagos, ƙarƙashin jagorancin Mr. Odife.
Ziyarar ta kasance wata dama ta fahimtar ci gaban da duniya ke samu a fannin binciken sararin samaniya.
Sarki Sanusi II ya halarci liyafa a Amurka
A ranar Asabar, 17 ga Mayu, sarkin ya kasance bako na musamman a liyafar dare da reshen ƙungiyar tsofaffin daliban King's College ta Arewacin Amurka suka shirya a birnin Houston.
Liyafar ta samu halartar fitattun mutane da suka haɗa da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da Dr Oluyinka Olutoye, likitan da ya yi fice a duniya.
Dr Oluyinka Olutoye ya yi fice a aikin tiyata matuka, inda ya taba cire jariri a cikin mahaifiyarsa kuma ya mayar da shi.
Ziyarar sarkin ta bar tarihi a zukatan ‘yan Nigeria mazauna Houston da kuma abokansa na King's College, suka bayyana farin cikinsu da haduwa da shi a waje.

Asali: Facebook
Kafin tafiyarsa zuwa Amurka, Sarkin ya jagoranci taron kaddamar da jirgin farko da ya dauki alhazan jihar Kano zuwa aikin Hajji.
Saraki ya yi bayani a wani taro a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya yi magana a wani taro a Amurka da Sanusi Ii ya halarta.
Bukola Saraki ya bayyana yadda aka samu sabani tsakaninsa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a wajen taron.
Saraki ya koka da yadda ya gaza samun goyon bayan 'yan Najeriya a lokacin, wanda ya ce hakan ya yi tasiri a majalisun da suka biyo baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng