'Dan Majalisar NNPP, Kofa Ya Fadi Matsayarsa kan Neman Kujerar Gwamnan Kano

'Dan Majalisar NNPP, Kofa Ya Fadi Matsayarsa kan Neman Kujerar Gwamnan Kano

  • 'Dan majalisar NNPP, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ba shi da sha’awar kujerar gwamna ko sanata a zaben 2027 mai zuwa
  • Ya ce amma yana kallon masu yi masa wannan kira a matsayin girmamawa da kuma gamsuwa da gudunmawar da ya ke bayarwa a siyasa
  • Hon. AbdulMumin Kofa ya kara da cewa burinsa ya fi karfi a wajen tallafa wa wasu su samu ci gaba fiye da neman manyan mukamai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa ba shi da niyya ko sha’awar tsayawa takarar gwamnan jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Kofa, wanda shi ne shugaban kwamitin gidaje da muhalli na majalisar, ya ce haka kuma ba shi da aniyar neman kujerar Sanata.

Hon Kofa
Dan majalisar NNPP ya yi martani kan zargin zai nemi gwamna ko Sanata a Kano Hoton: AbdulMumin Jibrin
Asali: Facebook

Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana haka ne ta cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 18 ga Mayu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Kofa ya magantu kan neman takara

Hon. Kofa ya bayyana cewa magoya baya da sauran jama'a za su ji cikakken bayani kan batun neman takara idan lokacin yin hakan ya zo.

Ya kara da bayyana cewa:

“Ina jin tilas a kowane lokaci in maimaita cewa ba ni da niyyar tsayawa takarar Sanata daga Kano ta Kudu, balle ma gwamnan jihar Kano a shekarar 2027."

Ya ce yana ganin yawaitar jita-jitar da ke danganta shi da irin wadannan mukamai a matsayin wata alama ta girmamawa da karbuwa bisa gudunmawar da ya bayar a fagen siyasa da hidimar jama'a.

Hon Kofa ya ce:

“Ba abin mamaki ba ne idan sunana na ci gaba da fitowa a irin wadannan tattaunawa, na dauki hakan a matsayin yabo da girmamawa kan irin kokarin da na bayar a siyasa, kuma zan ci gaba da bayar da gudunmawa don ci gaban al’umma da kasa baki daya.”

'Kishin mutanen Kano ne a gaba na,' Kofa

Hon. Kofa ya ce duk da kasancewarsa dan majalisar wakilai karo na hudu, bai manta da burinsa na taimaka wa wasu su samu ci gaba a siyasance da ma na rayuwa ba.

Ya ce:

“Ko a wannan matsayi na yanzu a matsayin dan majalisa karo na hudu, da na lashe zabe a jam’iyyu daban-daban, har yanzu ina da burin taimaka wa wasu su samu rayuwa mai kyau."

Ya kuma lissafa irin manyan mukaman da ya rike a majalisar wakilai, daga ciki har da shugabancin kwamitoci kamar na kudi, kasafin kudi da sufuri.

Hon Kofa
Dan majalisar NNPP ya ce ba neman mukamai ne a gabansa ba Hoto: AbdulMumin Jibrin
Asali: Facebook

Haka kuma ya taba shugabantar kwamitin harkokin wajen kasashen duniya da na gidaje da muhalli, sannan ya taba zama darakta a Hukumar Raya Gidaje ta Tarayya (FHA).

Ya ce:

“Wanda ya san ni da kyau ya san cewa duk inda na samu kaina, ko a siyasa ko a harkokin kasuwanci da na fara kafin shiga siyasa, ko a fannin ilimi da sauransu, ina da kishin aiki da samar da sakamako. Wannan shi ne halayyata."

Hon. Kofa ya nemi afuwar mutanen Kano

A wani labarin, kun ji cewa Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya gyara kalamansa kan goyon bayan kudirin haraji.

Ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kudirin baki dayansa, yana mai jaddada cewa yana amfani da matsayinsa ne domin kare muradun mazabarsa, Arewa da kuma Najeriya gaba ɗaya.

Kalamansa na zuwa ne bayan jama'a sun fusata saboda nuna goyon baya ga kudirin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika ga majalisa kan tsarin haraji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.