Shettima, Atiku, Sarkin Musulmi, Dangote, Manyan Najeriya na Taron Tattali a Taraba
- Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilci Bola Tinubu a Taron Zuba Jari na Taraba
- Taron ya mayar da hankali kan bunkasa noma, makamashi, hakar ma’adanai da masana’antu a jihar
- Fitattun mutane da ’yan kasuwa daga ciki da wajen Najeriya sun halarci taron da ake gudanarwa Jalingo
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya isa birnin Jalingo domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron zuba jari da ake gudanarwa a Taraba a bana.
Taron na da nufin jawo hankalin masu zuba jari da masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki domin yin hadin gwiwa da jihar.

Asali: Twitter
Tun a kwanakin baya gwamnatin jihar Taraba ta bude shafin yanar gizo domin yin bayani kan lamuran da suka shafi taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya tara manyan ’yan kasuwa, ’yan siyasa da shugabanni daga sassa daban-daban na kasar, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Sarkin Musulmi.
Manyan Najeriya sun je taron tattali a Taraba
Taron ya zama wata dama ta musamman wajen nunawa duniya irin albarkatun da jihar Taraba ke da su musamman a fannin noma, makamashi da hakar ma’adanai
An bayyana cewa hakan na da tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin Arewa maso Gabas da ma kasa baki daya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da manyan ’yan kasuwa irinsu Alhaji Aliko Dangote da Tony Elumelu sun halarci taron.
Hadimin mataimakin shugaban kasa ya wallafa a X cewa Sanata Kashim Shettima na cikin masu jawabi wajen taron.
Me ake fata a taron tattali na Taraba?
An bayyana cewa babban muradin taron shi ne kirkiro hadin gwiwa tsakanin masu zuba jari da jihar domin samar da cigaba da zai dade yana amfani.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa Taraba na da arziki da dama da har yanzu ba a taba amfani da su yadda ya kamata ba, musamman a fannonin noma da makamashi da ma’adanai.
A lokacin taron aka samu halartar wasu gwamnoni irinsu Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago da mataimakin gwamnan Bauchi, da wasu ministoci daga gwamnatin tarayya.

Asali: Twitter
Taron ya kuma bai wa Taraba damar karfafa hulda da cibiyoyin ci gaba da bankuna, tare da jaddada cewa jihar na da ingantaccen yanayi da albarkatu don gina masana’antu.
Manyan da suka halarci taron sun hada da:
1. Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima (wakilin Shugaba Bola Ahmed Tinubu)
2. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar
3. Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago
4. Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, CFR
5. Shugaban Heirs Holdings, Tony Elumelu
6. Shugaban Dangote Group, Aliko Dangote
7. Wasu Ministocin Gwamnatin Tarayya
8. Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi
Dangote ya mallaki kamfani a Kenya
A wani rahoton, kun ji cewa attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya mallaki wani katafaren kamfani a Kenya.
Rahotanni sun nuna cewa Dangote ya mallaki kamfanin ne tare da wani abokin kasuwancinsa dan kasar Amurka.
Hakan na zuwa ne bayan mai kudin ya daura damarar samar da babban kamfanin sukari a kasar Ghana da ke Afrika ta Yamma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng