Gwamnan Sokoto Ya Bude Masallaci a Mahaifar Sheikh Gumi da Shehu Shagari
- Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da sabon masallacin Juma’a da aka gina a Shagari, garin da fitaccen malami Abubakar Gummi ya fito
- Ahmed Aliyu ya ce masallacin alama ce ta ci gaba da kishin addini da al’ada, tare da bukatar al’ummar yankin su kula da ginin dakin ibadan
- Taron ya samu halartar tsohon mataimakin gwamna, Barista Mukhtar Shagari, wanda ya nuna goyon bayansa ga ci gaban addini a Sokoto
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta ƙaddamar da sabon masallacin Juma’a da aka gina a garin Shagari.
Gwamna Ahmed Aliyu ya ce an dauki matakin ne a kokarin raya al’umma da kyautata ayyukan addini.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da gwamna Ahmed Aliyu ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masallacin da ke cikin garin da babban malamin addini Sheikh Abubakar Mahmud Gummi ya fito, na daga cikin wuraren ibada da ke da tarihi mai zurfi da kima a zukatan al’ummar Musulmi.
Taron kaddamarwar ya gudana cikin natsuwa da farin ciki, inda aka yaba wa gwamnatin jihar bisa jajircewar ta wajen haɗa ci gaban addini.
An kaddamar da masallaci a mahaifar Gumi
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa masallacin ba kawai wuri ne na ibada ba, har ila yau alama ce ta girmama al’adun Musulunci da suka yi fice a Sokoto da ma Najeriya gaba ɗaya.
Ya ce:
“Wannan masallaci alama ne ta jajircewarmu wajen gina al’umma mai tsari da kishin addini.
"Garin Shagari ya haifi babban malamai kamar Sheikh Abubakar Gummi, kuma masallacin zai ci gaba da kasancewa hanyar shiryarwa ga al’umma.”
Gwamnan ya gode wa tsohon mataimakin gwamna, Barista Mukhtar Shagari, wanda ya halarci taron kuma ya jagoranci kaddamar da masallacin.
Ahmed Aliyu ya ce halartar Barista Mukhtar Shagari ya nuna haɗin kai da kishin cigaban jihar Sokoto.

Asali: Twitter
An bukaci kula da masallacin mahaifar Gumi
Ahmed Aliyu ya bukaci shugabannin masallacin da mazauna yankin su kula da masallacin domin ya ci gaba da zama cibiyar hadin kai da ibada.
Gwamnan ya ce:
“Ina kira gare ku da ku tabbatar da tsafta da kula da wannan masallaci."
Ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da saka hannun jari a bangarori daban-daban na rayuwar al’umma, ciki har da bangaren addini.
Punch ta wallafa cewa gwamnan ya yaba wa 'yan Hisba bisa kokarin da suke a jihar yayin bude masallacin.
An kaddamar da manhajar Kur'ani a Madina
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta kaddamar da manhajar Kur'ani a yayin da ake kokarin fara aikin hajji.
Rahotanni sun nuna cewa manhajar da aka kaddamar ita ce mafi girma a duniya kuma za a amfana da ita.
Limamin harami, Sheikh Abdulrahman Sudais ne ya kaddamar da manhajar a masallacin Manzon Allah SAW a Madina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng