Dangote Ya Shiga cikin Jerin Manyan Attajirai 100 Masu Taimakon Bayin Allah
- Attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, ya shiga cikin jerin mutane 100 da suka fi bayar da gudummawa ga talakawa a duniya
- Dangote, wanda shi ne kadai dan Najeriya da ya shiga jerin, na kashe akalla dala miliyan 35 a kowace shekara wajen ayyukan jin kai
- Daga cikin ayyukansa akwai yaki da karancin abinci mai gina jiki, samar da alluran rigakafi da kuma zuba jari a bangaren ilimi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Aliko Dangote, shugaban shugaban rukunin kamfanin Dangote da gidauniyar Dangote ya samu shiga cikin jerin farko na mattijarai da ke taimakon talaka a duniya na shekarar 2025.
Dangote, ya shiga jerin jagorori 100 da ke da tasiri wajen aikin taimakon al’umma a duniya, kuma shi ne kadai dan Najeriya da ya samu shiga wannan gagarumin jerin.

Asali: Facebook
Mujallar nan ta Time Magazine ce ta wallafa jerin sunayen a ranar Talata, inda Aliko Dangote ya samu matsayi saboda ayyukan gidauniyarsa ya kai $35m a kowace shekara a fadin Afrika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kasance cikin jerin fitattun mutane da masu aikin jin kai da suka hada da Michael Bloomberg, Oprah Winfrey, Warren Buffett da Melinda Gates, wadanda aka saka a rukuni na musamman mai suna “Titans”.
Dangote: Jerin attajirai masu taimakon talaka
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin fitattun mutane a wannan jerin sun hada da David Beckham, Dolly Parton, Lisa Yang, Michael Dell da Susan Dell.
Sauran sun hada da Tsitsi da Strive Masiyiwa, Jack Ma, Alex Soros, Prince William da Catherine da Princess of Wales, wadanda aka yaba da ayyukansu na taimakon bil’adama.

Asali: Getty Images
An karrama jimillar mutane 100 daga kasashe 28 saboda kokarinsu a fannonin taimako a rukuni uku, Dangote ya shiga cikin mutane 23 da aka saka a rukunin “Titans”.
Rahoton ya ce Dangote na taimako da dukiyarsa da ta kai dala biliyan 23.9 ta hanyar saka hannun jari a bangarorin siminti, noma da tace man fetur a Najeriya.
Yadda Dangote ke taimakon talakawa
A shekarar 2014, Dangote ya ware dala biliyan 1.25 domin kafa gidauniyar Aliko Dangote da nufin taimakon nahiyar Afrika wacce ta taka rawar gani a nasarar da ya samu.
Gidauniyar na kashe kimanin dala miliyan 35 a kowace shekara wajen aiwatar da ayyuka a Najeriya da sauran kasashen Afirka.
A baya, Dangote ya ce:
“Zuba jari a fannin abinci mai gina jiki, lafiya, ilimi da habaka tattalin arziki na daga cikin gudummawarmu domin ganin 'yan Afrika sun samu nasara.”
Daga cikin ayyukan gidauniyar da ke gudana yanzu akwai wani shiri na dala miliyan 100 da zai gudana tsawon shekaru da dama domin yakar matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
Haka kuma, gidauniyar ta fara wani shiri na rigakafin cututtuka a Najeriya tare da hadin gwiwa da gidauniya Bill da Melinda Gates da don kawar da matsalolin da ake fuskanta.
A kwanan nan, Dangote ya bada gudummawar dala miliyan 10 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Jihar Kano da sauransu.
Dangote ya sake rage kudin fetur
A baya, mun wallafa cewa kamfanin matatar mai na Dangote ya sanar da sabon rangwame a farashin litar man fetur daga N835 zuwa N825, a wani yunƙuri na ƙara janyo hankalin jama'a.
Rahotanni sun nuna cewa wannan rage farashin na zuwa ne makonni kaɗan bayan da kamfanin ya saukar da farashin daga N865 zuwa N835 a watan da ya gabata.
An gano cewa sabon sauyin farashin wani mataki ne da matatar Dangote ke ɗauka don saukakawa abokan cinikinta da kuma nuna ƙarfin ta a kasuwar mai ta cikin gida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng