Wata Sabuwa: Ma'aikata Sun Yi Gangami a Abuja, Sun Rufe Ofishin Ministan Kudi
- Fusatattun ma'aikatan hukumar nukiliya sun rufe hedikwatar ma'aikatar kudi saboda rashin biyan alawus da bashin albashin wata biyu
- Ma'aikatan sun zargi ministan kudi, Wale Edun da hana su hakkokinsu duk da roƙo da suka yi, inda suka bayyana cewa sun gaji da yin haƙuri
- Sun ce gwamnati na karɓar duk kuɗin da hukumar ke samu maimakon barin wani kaso, lamarin da ya hana su samun albashin watannin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wasu ma’aikatan hukumar kula da harkokin nukiliya ta Najeriya sun rufe hedikwatar ma’aikatar kudi ta tarayya da ke Abuja a ranar Talata.
An ce fusatattun ma'aikatan sun rufe hedikwatar, wacce ke dauke da ofishin ministan kudi, saboda rashin biyan bashin alawus da sauran hakkokinsu na albashi.

Asali: Twitter
Ma'aikatan nukiliya sun yi gangami a Abuja
Jaridar The Cable ta rahoto cewa ma'aikatan sun yi zanga zangar ne a ƙarƙashin ƙungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatan sun zargi ministan kudi, Wale Edun, da hana su hakkokin da doka ta tanada duk da roƙon da suka yi sau da dama.
Sanye da jajayen riguna, ma'aikatan sun rika rera waƙoƙi da ke nuna haɗin kai kan matakin da suka dauka, yayin da suka toshe ƙofar shiga ma’aikatar, wanda ya hana shige da ficen ababen hawa.
An ruwaito cewa masu zanga zanga sun rike kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce kamar haka: “Wale Edun, ka biya mu alawus ɗinmu.”
Sauran rubutun sun hada da: "A bar talaka ya sha iska," "A daina jan kafa, a biya mu hakkokinmu kawai," da dai sauransu.
Ma'aikata sun rufe kofofin ma'aikatar kudi
Ɗaya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, wanda ya nemi a sakaya sunansa ba, ya shaida wa wakilin jaridar Punch cewa wannan mataki na daga wata takaddama da ta samo asali tun 10 ga Fabrairu, 2025.
A cewarsa:
“Wannan zanga-zangar ta kin amincewa da cin kashin da ake yi mana ce. A yau mun rufe wasu ƙofofi kawai, amma gobe babu wanda zai shiga ko ya fita daga ginin.”
Ya ce mambobinsu da ke aiki a hukumar kula da harkokin nukiliya ta Najeriya ba su samu alawus da wasu hakkokin su ba, inda wasu har yanzu suke bin bashin albashin Maris da Afrilu.
"Tun muna yi masu tuni, muka dawo muna roƙo, amma ministan ya ƙi ɗaukar mataki, an banzatar da walwalar ma'aikatan, an hana su hakkokinsu” inji jagoran.

Asali: Twitter
Ana zargin minista da rike kudin ma'aikata
Ya zargi gwamnatin tarayya da ci gaba da karɓar kashi 100 cikin 100 na kuɗaɗen da hukumar ke samarwa da kanta, maimakon barin kashi 50 kamar yadda doka ta tanada, lamarin da ke rage wa hukumar damar biyan hakkokin ma’aikata.
Ya kara da cewa:
“Ba wai hana ma'aikata alawus kawai gwamnati take yi ba, har ma da toshe kuɗaɗen gudanar da aiki. Wannan ya sa muka ɗauki wannan mataki.
Kokarin jin ta bakin ma’aikatar kudi bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, yayin da daraktan yaɗa labaran ma’aikatar, Mohammed Manga, ya tura 'yan jarida zuwa fadar shugaban kasa domin samun martani.
Za a samar da lantarki ta hanyar nukiliya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban cibiyar makamashin nukiliya, Farfesa Yusuf Aminu Ahmed, ya ce Najeriya na dab da fara samar da lantarki ta hanyar nukiliya.
Ya bayyana wannan babban kuduri na gwamnati a taron makamashi da aka gudanar a jihar Kaduna, a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu, 2025.
Farfesa Yusuf Aminu Ahmed ya ce duk shirye-shiryen aikin sun kammala, amma ana jiran umarnin karshe daga shugaban kasa kafin a kaddamar da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng