Abin da Gwamnati Ta ke Yi da Kudin da Aka Karbo daga Hannun Barayi Inji EFCC

Abin da Gwamnati Ta ke Yi da Kudin da Aka Karbo daga Hannun Barayi Inji EFCC

  • Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da cewa ta kwato sama da Naira biliyan 50 daga hannun barayin gwamnati
  • Hukumar ta ce wannan yana daga cikin kuɗaɗen da aka zuba a Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) don tallafawa dalibai
  • EFCC ta bayyana cewa shekarar 2024 ita ce ta fi kowace shekara yawan kuɗaɗen da aka kwato tun kafuwar hukumar a 2003

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ce ta kwato sama da Naira biliyan 50 daga hannun masu aikata zamba a shekarar 2024.

Ta bayyana cewa wannan kudi yana daga cikin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta zuba a Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) don tallafawa dalibai.

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

Hukumar EFCC
EFCC ta kwato manyan kudade daga barayin gwamnati Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wannan bayani ya fito ne daga rahoton kididdiga na EFCC na shekarar 2024 da aka gabatar wa manema labarai ranar Lahadi a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati: "Nasarorin da EFCC ta samu"

Rahoton Nigerian Tribune ya ce hukumar EFCC ta bayyana ayyukanta na shekarar 2024 a matsayin manyan nasarori a yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.

EFCC ta ce wannan shekarar ita ce ta fi kowace shekara yawan kuɗaɗen da aka kwato tun lokacin kafuwarta a shekarar 2003 daga hannun barayin gwamnati.

Hukumar EFCC ta kwato kuɗin gwamnati

Kididdiga ta nuna cewa Naira biliyan 50 da gwamnatin tarayya ta ba NELFUND an samo su ne daga kuɗin da EFCC ta kwato.

Hukuma
EFCC ta mika kudin da aka kwato ga gwamnati Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Twitter

EFCC ta ce:

"Waɗannan kuɗin sun haɗa da Naira biliyan 364.6; Dalar Amurka miliyan 214.51; Yuro 54,319; Yuro 31,265; Dalar Kanada (CAD) 2,990 da Dalar Ostareliya (AUD) 740.00."

Kara karanta wannan

An sha mamaki da EFCC ta yi wa'azi da Kur'ani kan rashawa a Najeriya

"Sauran sun haɗa da: Kudin Faransa (CFA) 7,821,375, Dirham na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) 170, Riyal na Saudiyya 5,115, Yen na Japan W73,000,105, Cedi na Ghana (GH¢) 225 da Rand na Afirka ta Kudu 50,000."

Yadda EFCC ta taimaka wa gwamnati

A cewar hukumar EFCC, wasu daga cikin kuɗin da ta kwato an sake zuba su ne a cikin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa don amfanin jama'a.

Hukumar ta danganta nasarorinta ga jajircewar jami'anta da kuma yanayin aiki mai kyau da shugabanci da masu ruwa da tsaki suka samar.

Gwamnati ta yi nasarar tura wasu kurkuku

EFCC ta ce an yi nasara wajen yanke hukunci a kan mutane 4,111 a shekarar 2024, wanda ya fi yawa a tarihin shekaru 22 na hukumar.

An samu wannan nasara ne daga korafe-korafe 15,724, bincike 12,928, da kuma shari'o'i 5,083 da hukumar ta yi da masu lalata tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Tsohuwar ministar Tinubu ta kwana a hannun EFCC kan zargin karkatar da N138m

EFCC: "Uju ta wawashe kudin gwamnati"

A wani labarin, kun ji cewa tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy Ohanenye, ta kwana a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) kan zargin almundahanar kudi.

Wannan lamarin na zuwa ne bayan da EFCC ta fara bincike kan zargin da ake yi mata na karkatar da kuɗi da kuma saba ka’idojin sayen kayan gwamnati lokacin da take shugabantar ma’aikatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng