Gwamna Uba Sani Ya Kwace Kudaden Kananan Hukumomi? ALGON Ta Yi Bayani
- Wani rahoto ya yi yawo mai zargin cewa Gwamna Uba Sani ya kwace kudaden kananan hukumomi inda yake tsakura masu wani kaso dan kadan
- Rahoton ya nuna cewa abin da gwamnan yake tsakurawa kananan hukumomin bai wuce N25m a kowane wata
- Kungiyar shugabannin kananan hukumomi Najeriya (ALGON) reshen jihar Kaduna ta fito ta yi martani kan rahoton wanda aka yada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Ƙungiyar shugabannin kananan hukumomin Najeriya (ALGON), reshen jihar Kaduna, ta yi martani kan rahoton cewa Gwamna Uba Sani ya kwace kudadensu.
Kungiyar ALGON ta yi watsi da rahoton wanda ke zargin cewa Gwamna Uba Sani, ya ƙwace kudaden rabon ƙananan hukumomi na jihar, inda ta siffanta shi da na ƙarya, mai cike da maƙarƙashiya.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ALGON na jihar, Hon. Jamilu Abubakar, ya fitar a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026.
Me ALGON ta ce kan zargin?
Hon. Jamilu Abubakar ya bayyana rahoton a matsayin gangancin karkatar da gaskiya da aka tsara domin yaudarar al’umma, da kuma raunana kwarin gwiwa ga sauye-sauyen da ake gudanarwa a halin yanzu a cikin tsarin ƙananan hukumomin jihar.
A cewarsa, jihar Kaduna ta kasance ɗaya daga cikin ƴan jihohi kalilan a cikin tarayyar ƙasar da suka nuna jajircewa ta gaske ga ƴancin ƙananan hukumomi, da kuma lissafin gudanar da kuɗaɗen gwamnati.
“Zargin cewa ana karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi ko kuma an ƙwace su, ba shi da wani tushe kuma ba shi da wata sahihiyar shaida."
“Ƙananan hukumomi a jihar Kaduna su da kansu suke gudanar da biyan albashi, fansho, da sauran nauye-nauye na doka ta hanyar tsarin biyan kuɗi na intanet cikin cikakken bin umarnin hukuncin Kotun Ƙoli a kan ƴancin ƙananan hukumomi.”
- Hon. Jamilu Abubakar
Shin ana ba da N25m duk wata?
Kungiyar ta kuma yi watsi da iƙirarin ƙirƙira da ke cewa majalisun ƙananan hukumomi suna karɓar N25m kawai a matsayin kuɗaɗen rabon kowane wata, inda ta bayyana wannan zargi a matsayin mai yaudara kuma mara mutunci, jaridar The Sun ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan
Jonathan zai yi takarar shugaban kasa a inuwar PDP a 2027? Hadiminsa ya yi bayani
Haka zalika, ƙungiyar ta ƙaryata iƙirarin cewa shugabannin ƙananan hukumomin sun gudu sun bar mazaɓunsu, inda ta jaddada cewa jami’an cikin gida suna ci gaba da tattaunawa da al’ummominsu ta hanyar shawara akai-akai da kuma tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi.

Source: Twitter
ALGON ta ƙalubalanci shafin labaran na intanet ɗin da kuma majiyoyin da ba a bayyana sunansu ba da aka ambata a cikin rahoton da su samar da hujjoji na gani da ido don goyon bayan zarge-zargen, yayin da ta buƙaci a gaggauta janye rahoton a bainar jama'a tare da ba da haƙuri a cikin sa'o'i 48.
Uba Sani ya nada Sarkin Kagarko
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya nada sarkin Kagarko da ke a ƙaramar hukumar Kagarko.
Gwamna Uba Sani ya amince da nadin Suleiman Sa’ad Abubakar a matsayin sabon Sarkin Kagarko da ke karamar hukumar Kagarko a Kudancin jihar Kaduna.
Sabon sarkin, wanda kafin yanzu yake riƙe da sarautar San Turakin Kagarko, ya gaji marigayi Sa’ad Abubakar wanda ya rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
