Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Sabon Shugaban Hukumar JAMB

Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Sabon Shugaban Hukumar JAMB

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugav'ban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB).

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Farfesa Aina zai maye gurbin Farfesa Ishaq Oloyede wanda wa’adinsa na biyu zai kare ranar 31 ga watan Yulin 2026.

Segun Aina.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu a takardu, da sabon shugaban JAMB, Farfesa Segun Aina Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin ya labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da naɗin a shafinsa na X a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu, 2026.

Sakamakon haka ne Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwa biyar da ya kamata a sani game da sabon shugaban JAMB, ga su kamar haka.

1. Farfesa a fannin Injiniyancin Kwamfuta

Segun Aina malami ne a fannin Injiniyan Kwamfuta a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife a jihar Osun, kuma ya kai har matsayin Farfesa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya zakulo matashi ɗan shekara 40 ya naɗa shi sabon shugaban hukumar JAMB

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana kallonsa a matsayin ƙwararren masani a harkokin tsara jarabawa, fasahar zamani da sauya fasalin cibiyoyi.

2. Aina ya yi karatu a Birtaniya

Farfesa Aina ya samu digirin farko a fannin Computer Systems Engineering daga Jami’ar Kent da ke Birtaniya.

Haka kuma ya yi digiri na biyu da digirin Ph.D a fannonin Internet Computing and Network Security da Digital Signal Processing daga Jami’ar Loughborough ta kasar Birtaniya.

Baya ga haka, ya halarci shirin horas da manyan jami’ai a Lagos Business School a nan gida Najeriya.

3. Ya fara aiki da JAMB tun lokacin NYSC

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Aina ya fara hulɗa da JAMB ne tun lokacin bautar kasa ta NYSC, inda ya samu gogewa a harkokin ba ɗalibai guraben karatu da tsarin sarrafa bayanai.

An ce wannan gogewa ta taimaka wajen gina gudummawar da ya bayar daga baya a gyaran tsarin jarabawa da inganta ayyuka a hukumar

4. Ya yi aiki da manyan hukumomi

Da fiye da shekaru 15 na gogewa bayan kammala karatu, Aina ya yi aiki da manyan hukumomin jarabawa irin su NECO da NABTEB da kuma ma’aikatun ilimi na jihohi daban-daban.

Kara karanta wannan

Tana ƙasar waje: Lauyan Sadiya Farouk ya fadi abin da ya hana ta zuwa kotu

Kwarewarsa ta haɗa da gogewar da ya samu a fannin fasahar ICT, tabbatar da sahihancin jarabawa, sauya tsarin aiki zuwa na zamani da kuma gyaran fasalin gudanarwa.

Segun Aina.
Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa (JAMB), Farfesa Segun Aina Hoto: OAU News Update
Source: UGC

5. Zai kafa tarihin a hukumar JAMB

Farfesa Aina, wanda zai cika shekaru 40 a watan Yuli, na daga cikin matasan farfesoshi a fannin Injiniyan Kwamfuta a Najeriya.

Yanzu haka zai kafa tarihi a matsayin shugaban hukumar JAMB mafi ƙarancin shekaru tun da aka kafa hukumar.

Ya kasance mamba a ƙungiyoyi injiniyoyi masu zaman kansu da suka haɗa da COREN, NSE, IEEE da IET.

JAMB ta kayyade makin shiga jami'o'i

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar JAMB ta kayyade maki 150 a matsayin mafi karanci ga wadanda ke neman gurbin shiga jami'o'i a shekerar 2026 a Najeriya.

Hukumar ta kuma bayyana maki 150 a matsayin mafi karancin makin.shiga kwalejojin jinya, yayin da na kwalejojin fasaha ya kasance maki 100 cikin maki 400 na jarabawar UTME.

Hukuma JAMB ta sanar da hakan ne a taron tsara manufofin shiga makarantu na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262