Cutar Daji Mai Karfi Ta Kama Tsohon Shugaban Amurka, Joe Biden bayan Barin Ofis

Cutar Daji Mai Karfi Ta Kama Tsohon Shugaban Amurka, Joe Biden bayan Barin Ofis

  • Likitoci a kasar Amurka sun gano cewa tsohon shugaban ƙasar, Joe Biden na fama da ciwon daji wanda ya bazu zuwa ƙasusuwansa.
  • Kafin a bayyana cewa yana dauke da cutar a ranar Lahadi, Amurkawa sun bayyana damuwa kan lafiya da karfin jikinsa a lokacin yana shugaba
  • Manyan shugabanni kamar Donald Trump, Kamala Harris, da Barack Obama sun bayyana tausayinsu tare da fatan zai samu samu sauki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar America – Ofishin tsohon shugaban ƙasar Amurka, ya tabbatar da cewa Joe Biden na fama da wani nau'in ciwon daji mai tsanani wanda ya bazu zuwa ƙasusuwansa.

Likitoci sun gano cewa Biden, wanda ke da shekaru 82, na dauke da cutar dajin bayan sun gano wani kumburi a jikinsa.

Biden
An bayyana cewa cutar daji ta kama tsohon shugaban Amurka Hoto: Joe Biden
Asali: Facebook

Tashar Aljazeera ta bayyana cewa an kai Biden asibiti bayan ya fara fama da yawaitar fitsari, wanda ake ganin yana bukatar ganin likita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hoe Biden na fama da cutar daji

BBC ta wallafa cewa shekarun Joe Biden da lafiyarsa sun kasance abin damuwa ga masu kada kuri’a a lokacin da yake kan mulki a matsayin shugaban ƙasa, wanda ya hana shi sake tsayawa takara.

Biden
Cutar daji ta bazu zuwa kasusuwan tsohon shugaban Amurka Hoto: Joe Biden
Asali: Facebook

Amma sanarwar da Ofishinsa ya fitar a ranar Lahadi, an ce:

“Ko da yake wannan nau’in cutar daji yana da tsanani, yana karbar magungunan daidaita wasu sinadarai a jiki, wanda hakan yana baiwa likitoci damar samun sauƙin kula da ita.”
“Shugaban ƙasa da iyalinsa na tattaunawa da likitocinsa kan hanyoyin magani da za su bi.”

Shugabanni sun fara taya Biden jaje

Donald Trump, wanda babban mai adawa da Biden ne, ya ce ya ji ba dadi da jin wannan labari, ya ce shi da uwargidansa na fatan tsohon shugaban ya samu sauƙi a cikin gaggawa.

Kamala Harris, wadda ta kasance mataimakiyarsa a lokacin mulkinsa, ta bayyana cewa ita da iyalinta na taya iyalan Biden addu’a.

Ta ce:

“Joe jarumi ne – kuma na san zai fuskanci wannan ƙalubale da ƙarfin hali, juriya, da kuma kyakkyawar fata kamar yadda ya saba a rayuwarsa da shugabancinsa."s

Tsohon shugaban ƙasar Amurka Barack Obama, ya nuna alhinin sa tare da yabawa ƙoƙarin da Biden ke yi na ganin an samu sababbin hanyoyin warkar da cutar daji.

Ya ce:

“Babu wanda ya fi Joe ƙoƙari wajen nemo hanyoyin magance duk wani nau'in ciwon daji, kuma ina da tabbacin cewa zai fuskanci wannan ƙalubale da ƙarfin zuciya da kima kamar yadda ya saba.”

Amurka ta ki shiga tsakanin Iran da Isra'ila

A baya, mun wallafa cewa tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta shiga rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ba.

Wannan na zuwa ne bayan kai harin ramuwar gayya da Iran ta yi a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu, 2024 sai dai Isra'ila ta ce ta kakkabe da yawa daga cikin jiragen da Iran ta aika mata.

Gwamnatin Amurka, wacce ta yabi Isra'ila ta ce sojojinta ba za su shiga fadan da ke tsakanin Iran da gwamnatin Benjamin Netanyahu ba, duk da kasancewarsu cikin haɗin gwiwa wajen kare yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.