Duniya ba Komai ba: Tsohon Gwamnan Katsina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi jimamin rasuwar tsohon gwamnan wanda ya mulki jihar tsakanin 1998 zuwa 1999 a lokacin mulkin soja
- Radda ya ce marigayin ya hada Katsina da Benue zumunci mai karfi da mutuwa ba za ta iya katsewa ba, ya yaba da gudunmawar da ya bayar
- Ya mika ta’aziyya ga Gwamna Hyacinth Alia da iyalan marigayin, yana cewa Kanal Akaagerger ya bar kyakkyawan tarihi na gaskiya da hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Jihar Katsina ta sanar da babban rashi da ta yi na mutuwar tsohon gwamnanta a Najeriya bayan fama da jinya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Kanal Joseph Iorshagher Akaagerger wanda ya mulki jihar ya riga mu gidan gaskiya.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamna Dikko Umaru Radda ya wallafa a Facebook a jiya Litinin 19 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin marigayi Kanal Joseph Akaagerger
An haifi marigayin a ranar 5 ga Mayu, 1956, kuma ya rike kujerar Sanata mai wakiltar Benue ta Arewa maso Gabas a shekarar 2007.
Joseph Akaagerger, wanda tsohon sanata ne daga yankin Benue ta Arewa maso Gabas kuma tsohon shugaban soja, ya rasu yana da shekaru 69.
Marigayin ya wakilci yankin a majalisar dokoki ta kasa daga 2007 zuwa 2011 a jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Gwamna Radda ya yi jimamin mutuwar marigayin
A cikin sanarwar, Ibrahim Kaula Mohammed ya ce Gwamna Radda, ya bayyana bakin cikinsa kan rasuwar marigayin.
Marigayin Kanal Akaagerger ya shugabanci Katsina daga 1998 zuwa 1999, lokacin mulkin soja, ya ba da gudummawa sosai.
Gwamna Radda ya ce marigayin ya kasance ginshiki na hadin kai tsakanin Katsina da Benue.
Sanarwar ta ce:
“Ina tuna yadda ya gina alaka da ta hada zumunci tsakanin jihohinmu; wannan zumunci har yau yana nan daram.
“Ba wai tsohon shugaba kawai muke makoki ba, amma muna kukan dan’uwa wanda ya hada mu zumunci.”

Asali: Original
Gudunmawar da marigayin ya bayar a Najeriya
Gwamna ya bayyana shi a matsayin mutum mai kwazo da fahimtar shari’a da kishin dimokuradiyya mara misaltuwa.
Ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue da iyalan marigayin, yana mai cewa ya zama dan Katsina ta wajen hidima.
Ya kara da cewa:
“Yayin da muke bankwana da wannan jarumi mai gaskiya da rikon amana, muna addu’ar Allah ya gafarta masa kuma ya karfafi iyalansa."
Yadda ake samar da gwamna a milkin soja
A lokacin mulkin soja a Najeriya, an saba nada gwamnonin sojoji wadanda ba lallai su kasance 'yan jiha ba kafin su zama gwamna.
Wannan tsarin ya bambanta da tsarin dimokuradiyya inda ake zaben gwamna kai tsaye daga cikin 'yan jihar da ke yake son mulki ta hanyar siyasa.
A mulkin soja, soja ne ke daukar nauyin mulki a jihohi, don haka sojojin da aka nada su zama gwamnonin jihohi galibi suna daga cikin manyan jami’an soji da aka tura daga wurare daban-daban na kasar domin shugabantar jihohi.
Dalilin wannan tsarin shi ne domin tabbatar da ikon soja a fadin kasa baki daya, sannan a rage yiwuwar tashin hankali na siyasa ko rikici na kabilanci da na yankuna.
Fa'idar hakan ga mulkin soja
Wannan ya ba gwamnatin soja damar sa ido da tsari a jihohi cikin sauki, ta hanyar nada mutanen da suka dogara da su kuma suke aiki da umarnin rundunar soja.
Haka kuma, an ga cewa wannan tsari yana haifar da hadin kai tsakanin jihohi daban-daban, saboda a kan nada soja daga wata jiha zuwa wata, wanda hakan ke taimakawa wajen rarraba alhakin shugabanci da rage tasirin son kai ko nuna bambanci tsakanin kabilu da yankuna.
Duk da haka, akwai masu suka kan wannan tsari, musamman wajen rashin damawa da al’ummar jiha kai tsaye wajen zaben shugabannin su, wanda ya saba wa tsarin dimokuradiyya.
Saboda haka, mulkin soja da tsarin nadin gwamnonin soja wadanda ba 'yan jiha ba, yana da nasa kalubale, amma yana da tasiri wajen daidaita ikon mulki a kasa a lokacin da aka yi amfani da shi.
Ta'addanci: Makudan kudi da gwamnatin Katsina ta kashe
Mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi magana kan maƙudan biliyoyin da ta kashe wajen yin fito na fito da matsalar rashin tsaro.
Mataimakin gwamnan Katsina, ya bayyana cewa ayyukan samar da tsaro a jihar sun laƙume maƙudan kuɗi har N36.8bn domin dawo da zaman lafiya a jihar.
Faruk Lawal Jobe ya bayyana cewa an kashe dukiyar wajen samar da rundunar tsaro, sayo kayan aiki da sauransu domin kakkaɓe ƴan bindiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng