Babban Malami Ya Rasu a Wurin Buga Wasanni, Abin da Ya Faru Ya Tada Hankalin Jama'a
- An shiga tashin hankali a jihar Anambra da limamin cocin Katolika ta Awka, Rabaran Anthony Udogu ya mutu a wurin wasanni
- A wata sanarwa da cocin ta fitar, ta bayyana cewa limamin ya mutu ne bayan ya faɗi yana tsaka da buga kwallon tennis da safiyar Talata
- Sanarwar ta miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa da daukacin mabiya cocin da yake jagoranta, ta ce za a sanar da tsare-tsaren jana'iza nan gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Awaka, jihar Anambra - Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a Awka, Jihar Anambra, da wani babban limamin coci ya riga mu gidan gaskiya a wurin wasanni.
Rabaran Anthony Udogu na Cocin Katolika da ke Awka ya fadi ya rasu yayin da yake wasan kwallon tennis a harabar St. Patrick, lamarin da ya tada hankulan jama'a.

Asali: Original
Vanguard ta ce rasuwar bazata da limamin ya yi a wurin wasan kwallon tennis ta tayar da hankulan mazauna yankin musamman mabiya ɗarikar Katolika a jihar Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cocin Katolika ya tabbatar da lamarin
Mai kula da harkokin cocin Katolika da ke Awka, Rabaran Charles Ndubuisi ya tabbatar da mutuwar limamin a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce:
"Cikin imani da gaskata dawowar Yesu Kristi nan gaba, Cocin Katolika ta Awka na sanar da rasuwar dan’uwanmu liman, Rabaran Anthony Udogu, wanda Allah ya karbi ransa a safiyar yau (Talata, 20 ga watan Mayu)."
Ta ya babban malamin ya mutu a wurin wasanni?
Sanarwar ta yi bayanin cewa babban limamin ya yanke jiki ya faɗi sumamme yana tsaka da buga ƙwallon tennis, kuma nan take aka garzaya da shi asibiti mafi kusa.
Sai dai a cewar sanarwa, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceto rayuwarsa, limamin ya cika a gadon asibiti.
Kafin rasuwarsa, Rabaran Udogu shi ne limamin cocin St. Francis of Assisi da ke Awka, kuma shi ne shugaban Awka Deanery II.
An san maragayin da kishi da ƙoƙari a duk abin da ya shafi aikin Ubangiji, shugabanci nagari da kuma ci gaban al’umma, kamar yadda Punch ta rahoto.

Asali: UGC
An fara mika sakon ta'aziyya ga iyalansa
Cocin Katolika ta mika ta’aziyyarta ga iyalinsa, ’yan cocinsa da duk masu jimamin rasuwarsa, tare da tabbatar da cewa za a fitar da cikakken bayani kan jana’iza nan gaba.
Sanarwar ta ƙare da cewa:
“Allah ya jiƙan Rabaran. Fr. Anthony Nnaemeka Udogu, ya kuma ba shi hutu cikin aminci a bisa ƙaunar Ubangiji.”
Malamai da nishadi a Najeriya
A cikin al’ummar Najeriya, malaman addini na da matsayi na musamman wanda ya bambanta su da sauran jama’a, musamman wajen gujewa harkokin nishadi na yau da kullum.
Tun ba yau ba, ana kallon malamai a matsayin jagorori kuma ginshikan tarbiyya da koyarwa a cikin al’umma.
Saboda wannan matsayi, su kan nisanci abubuwan da ba su dace da matsayin su ba kamar shiga wasanni ko abubuwan nishadi da ake ganin ba su da alaka da addini ko kuma wadanda za su iya rage darajarsu a idon jama’a.
Wannan ba yana nufin ba su jin dadin rayuwa ba ne, sai dai suna taka tsantsan wajen bayyana kansu a fili don zama abin koyi.
Ribar hakan ga malamai
Har ila yau, wannan halaye na malamai yana taimakawa wajen tabbatar da tsarkin dabi’u da inganta martabar addini a cikin al’umma.
Malamai su kan zama misalai na gaskiya, tsoron Allah, da kuma kiyaye al’adu na gari wanda ke jan hankalin mabiyansu zuwa ga kyawawan dabi’u da zamantakewa ta gari.
A wasu lokuta, musamman a yankuna masu tsananin bin addini, an fi ganin cewa malamai su ne ke da hakkin kiyaye mutunci da darajar al’umma ta hanyar nisantar abubuwan da za su iya kawo rikici ko fassara mara kyau.
Akasin hangen al'umma
Sai dai a wasu lokuta kuma, wasu malamai na iya shiga harkokin nishadi cikin takatsantsan ko kuma a lokutan da suka dace, musamman idan hakan zai taimaka wajen kusantar da jama’a ko inganta zumunci tsakanin mabiyansu.
Amma gaba ɗaya, a Najeriya da wasu kasashen Afirka, ana ganin malamai a matsayin mutane masu tsarkin hali da jigon al’umma, wadanda ba sa shiga harkokin nishadi kamar sauran mutane saboda matsayinsu na jagoranci da abin koyi.
Wannan dabi’ar tana da nasaba da al’adu da addini da kuma bukatar tabbatar da tsari da daraja a cikin al’umma baki ɗaya.
Fasto ya musanta cewa akwai wuta da aljanna
A wani rahoton, kun ji cewa wanda ya kafa cocin 'Solid Rock Kingdom' a jihar Akwa Ibom, Fasto John Okoriko ya yi ikirarin cewa babu wuta da aljanna kamar yadda ake faɗa.
Faston cocin ya kalubalanci abin da Kiristoci suka yi imani da shi game da rayuwar lahira, ya ce babu wani wurin da ake kira aljanna ko wuta.
A cewarsa, ma’anar aljanna a cikin Littafin Yesu na nufin kasancewar Allah a rayuwar muminai, ba wani wuri da ke can sama ba.
Asali: Legit.ng