Oyedepo ya raba kayan aikin asibiti da tallafin kayan agaji a Legas da Ogun

Oyedepo ya raba kayan aikin asibiti da tallafin kayan agaji a Legas da Ogun

Shararren Malamin addinin Kirista, Bishof David Oyedepo, ya bada kayan asabiti da kuma kayan agaji domin taimakawa gwamnati wajen yaki da COVID-19.

David Oyedepo ya raba wadannan kaya ne a Jihohin Legas da Ogun kamar yadda mu ka samu labari a wani jawabi da shugaban cocin ns Winners’ Chapel ya fitar.

Bishof Oyedepo ya aikawa Manema labarai jawabin da ya yi ta bakin wani Jami’in cocinsa, Farfesa Sheriff Folarin. Daga cikin kayan da aka bada har da mota.

Malamin addinin ya bada gudumuwar motar kwana-kwana da kuma na’urar yin gwajin cutar COVID-19, da na’urorin auna zafin jikin mutum da dai sauransu.

Jawabin Attajirin Faston ya ce: “Za a bada kyautar wadannan motoci a jihar Legas da Ogun, domin inganta kokarin da ake yi na maganin cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Najeriya za ta kara sallamar wadanda su ka warke daga Coronavirus

Oyedepo ya raba kayan aikin asibiti da tallafin kayan agaji a Legas da Ogun
Fasto Oyedepo ya yi rabon kayan abinci saboda annobar COVID-19
Asali: UGC

Sauran kayan sun kunshi kwalaye 20 na safar hannu, kwalaye 10 na tsummar rufe fuska. Na’urar auna zafin jiki 40, rigunan kare kai 500 da wasu kayan aiki.”

Hari ila yau daga cikin wannan kaya akwai wasu kwalaye biyu na na’urar awon hawan jini da kuma wata na’urar zamani mai auna dankarewar jini a jikin ‘Dan Adam.

Bayan wadannan kayan asibiti akwai buhunan abinci. “Akwai buhuna 400 na shinkafa, buhuna 150 na wanke, buhuna 400 na Garin rogo da gorar man gyada 500.”

Farfesa Folarin da ya ke magana a madadin kungiyar cocin Living Faith Church, ya nuna cewa wannan shi ne gudumuwarsu ga gwamnatin Najeriya da marasa hali.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng